Ticker

Danmaliyo-Maliyo

6.98 Ɗanmaliyo-Maliyo

Wannan ma wasa ne da ‘yanmata ke yi. Yana kama da wasan Salamatu da aka yi bayani a sama. An fi gudanar da wasan da dare, sai a wasu lokuta da ba a rasa ba da ake yin sa da yamma ko hantsi. Mafi yawancin garuruwan ƙasar Hausa an san da wannan wasa. Sai dai yadda ake gudanar da shi kan ɗan bambanta sakamakon bambancin wuri da karin harshe da makamantansu. Akan yi wasan ne a dandali ko filin ƙofar gida.

6.98.1 Yadda Ake Wasan Ɗanmaliyo-maliyo

Yan wasa na jeruwa wuri ɗaya, haɗe da juna. Ɗaya daga ciki za ta kasance a gaba. Daga nan wacce take gaban ko dai ɗaya daga cikin ‘yan wasa za ta riƙa ba da waƙa saura suna amsawa. Yayin da ake wannan waƙa, yarinyar da take gaba za ta riƙa faɗowa saura. Su kuwa za su tallafe ta su miƙar da ita tsaye. Haka za a ci gaba da yi har sai an ƙare waƙar. Daga nan sai wata yarinyar ta koma gaba. A haka – a haka har kowacce daga cikinsu ta yi

6.98.2 Waƙar Wasan Ɗanmaliyo-maliyo

Jagora: Ɗanmaliyo-maliyo.

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Ɗanmaliyo nawa.

Y/Amshi: Maliyo!

Jagora: Ya tafi ina ne?

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Ya tafi Ilori?

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Ba zai dawo ba.

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Sai a watan gobe.

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Gobe da labari.

Y/Amshi: Maliyo!

 

Jagora: Jibi da labarai.

Y/Amshi: Maliyo!

6.98.3 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki da kuma nishaɗantarwa tsakanin ‘yanmata. Domin kuwa watan goben ya yi, kuma Ɗanmaliyo bai dawo daga Ilorin ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments