Ticker

Yau Na Zama Baran Mata

6.99 Yau Na Zama Baran Mata 

Wannan ma wasa ne na yara mata da ke cikin rukunin wasannin tashe. Kimanin yara uku zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Sai dai kayan aikin guda ɗaya ne kawai, wato tsintsiya. Ana buƙatar kayan aiki yayin da za a gudanar da shi. Sannan yana tafiya da waƙa. Kamar sauran wasannin tashe, ana gudanar da shi ne da dare.

6.99.1 Yadda Ake Wasa

Masu ɗaya daga cikin masu wasa za ta riƙe tsintsiya. Yayain da aka iso wurin tashe, za ta nemi wuri ta fara shara. Sannan za ta riƙa ba da waƙa saura kuma na amsawa. Ga yadda waƙar take:

Mai Shara: Yau na zama baran mata,

Amshi: Share musu gidan tsaf-tsaf.

 

Mai Shara: Yau na zama baran mata,

Amshi: Share musu ɗaki tsaf-tsaf.

 

Mai Shara: Yau na zama baran mata,

Amshi: Allah Na son tsafta.

 

Mai Shara: Yau na zama baran mata,

Amshi: Annabina son tsafta.

 

Mai Shara: Yau na zama baran mata,

Amshi: Lada kike samu kullum.

Haka za su ci gaba da yi har sai an sallame su.

6.99.2 Tsokaci

Wannan wasa na nuna muhimmancin tsafta da matsayinta a addinance. Yana nuni da cewa, tsafta ba wahalar banza ba ce, domin kuwa hanya ce ta samun lada.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments