Dundunge

    7.10 Dundunge

    Wannan wasan yara maza da mata duka suna yin sa. Kimanin yara goma zuwa sama da haka ne suka fi gudanar da wannan wasa. Yana cikin jerin wasannin da ba sa tafiya da waÆ™a. Sannan yana buÆ™atar kayan aiki yayin gudanarwa.

    7.10.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a wani keÉ“aÉ“É“en fili da ba safai mutane ke zirga-zirga cikinsa ba.

    ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko ma dadare, idan akwai farin wata.

    7.10.2 KayanAiki

    i. Æ˜yalle ko tsumma (domin rufe idanun dundunge)

    ii. Kara ko tsumagiya/bulaliya

    7.10.3 Yadda Ake Wasa

    Za a samu É—an wasa guda É—aya a rufe masa/mata idanu da Æ™yalle ko tsumma ko dai wani abu mai kama da wannan. Sannan za a ba shi kara ko tsumagiya ya riÆ™e a hannu. Wato dai zai kasance tamkar makaho.

    ÆŠaya daga cikin masu wasa kuma zai riÆ™e wannan kara ko tsumagiya, tamkar É—an jagora. Sunan wanda aka rufe wa ido dundunge. Mai masa jagora zai tambaye shi, yayin da shi kuma zai riÆ™a ba da amsa kamar haka:

    ÆŠan Jagora: Dundunge dundunge ka ci tuwo?

    Dundunge: Eh.

     

    ÆŠan Jagora: Dundunge ka sha ruwa?

    Dundunge: Eh.

     

    ÆŠan Jagora: Dundunge ka sha fura?

    Dundunge: Eh.

     

    ÆŠan Jagora: Dundunge ina nawa?

    Dundunge: Kare ya zubar!

     

    ÆŠan Jagora: To duk nan ‘ya’yana ne, kowa ka samu ka lafta, har da ni babbansu.

    Da zarar an zo wannan gaÉ“a, kowa zai watse da gudu. Har shi É—an jagoran ma zai kama gabansa. Daga nan dundunge kuwa zai riÆ™a bi yana laluÉ“awa da karansa. Duk wanda ya tarar, sai bugu. Su kuwa za su riÆ™a zagaya dundunge, wasu har zungurinsa za su riÆ™a yi suna faÉ—in:

    Kowa ka samu ka lafta,

    Kowa ka samu ka lafta!

    Wani abin lura a nan shi ne, tambayoyin da ke sama an yi su ne a matsayin wasan maza, wato dundunge namiji ne. Idan kuwa a yara mata ne ke gudanar da wasan, to jinsin zai koma namata.

    7.10.4 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaÉ—i ga yara. Sannan hanya ce da suke bi domin motsa jikinsu. Yara da ma dundunge sukan sha gudu yayin gudanar da wasan.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.