Tserel

    7.12 Tserel 

    Wannan ma wasa ne wanda yara maza da mata duka suna yi. Akan iya yin tseren tsakanin kimanin yara biyu kacal. Sai dai idan aka samu taron yara, abin ya fi armashi. Wasan ba ya tafiya da waÆ™a, duk da ma wani lokaci yara na yin kirari da zuga ga masu tserel saboda su dage kada a bar su a baya.

    7.12.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali da kuma makarantun boko.

    ii. Akan gudanar da wasan  da hantsi ko da yamma ko da dare.

    7.12.2 Yadda Ake Wasa

    Masu tserel za su jeru a layi É—aya. Sannan za su duÆ™a su kafa guiwowin Æ™afafunsu É—aÉ—É—aya a Æ™asa, su kuma dafa Æ™asa. Daga nan za a Æ™irga daga É—aya zuwa uku. Da zarar an kammala wannan Æ™irge yara za su ruga a nakare zuwa wurin taÉ“awa. Da zarar mutum ya taÉ“a zai yi Æ™oÆ™arin dawowa da gudu idan tserel É—in ‘yar zuwa da dawowa ce. Wanda ya riga dawowa duk shi ne na É—aya. Idan kuma ‘yar zuwa ce kawai, wanda ya riga taÉ“awa shi ne na É—aya.

    7.12.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. A makarantun boko ma akan haÉ—a wasanni da kuma gasanni da suka shafi tserel.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.