Ticker

Ba Za Ku Ga Tafiyar ‘Yata Ba

7.13 Ba Za Ku Ga Tafiyar ‘yata  Ba

Wannan ma wasa ne wanda yara maza da mata duk sun yi tarayya wurin gudanar da shi. Kimanin yara biyu zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Akan rera waƙa a cikin wasan. Sannan wasa ne da ke buƙatar kayan aiki.

7.13.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a gida ko wurin sauran yara ko dai wani wuri da yara suke taruwa.

ii. Akan gudanar da wasan da hantsi ko da yamma. Wasu lokuta akan yi da dare amma idan akwai farin wata mai haske sosai.

7.13.2 Kayan Aiki

i. Ƙasa

ii. Ƙaramin dutse (tsakuwa) a matsayin ‘ya

7.13.3 Yadda Ake Wasa

Mai wasa zai tara ƙasa a gabansa, sannan ya gara shi yadda zai yi layi a ƙasa, mai ɗan kauri. Daga nan zai sanya ‘yarsa daga farkon ƙasar ya dafe ta da manyan yatsun hannunsa na hagu da dama. Yatsun da kuma ‘yar za su kasance lulluɓe da wannan ƙasa yadda ba za a iya kallonsu ba. Daga nan zai riƙa tura wannan ‘ya da yatsun nasa tare da waƙa kamar haka:

Ba za ku ga tafiyar ‘yata ba,

Ba za ku ga dawowarta ba.

 

Ba za ku ga tafiyar ‘yata ba,

Ba za ku ga dawowarta ba. 

A yayin da yake haka zai shammaci sauran‘yan wasa ya bar ‘yar tasa a wani gaɓa. Zai kuma ci gaba da tafiya da yatsunsa tamkar ‘yar tana tare da shi. A haka har sai ya je ƙarshen ƙasar. Daga nan kuma zai fara rarraba ƙasar ta hanyar yin gewaye haɗe da juna. Wato dai zai raba ƙasar zuwa gida-gida. Yawan gidajen ya danganta da tsawon ƙasar. Za su iya kasancewa biyar ko shida ko ma sama da haka.

Da zarar ya ƙare, sai kuma abokin wasa ya canka. Zai yi hakan ta hanyar nuna wa tare da baje gidan da yake tunanin ‘yar tana ciki. Idan ya canka daidai, to shi zai yi tafiya. Idan kuwa ya faɗi, wadda ya fara tafiya ne zai ci gaba.

7.13.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar nitsuwa tare da amfani da hankali domin gano haƙiƙanin gidan da mai tafiya ya bar ‘yarsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments