O Maciji

    7.15 O Maciji 

    Wannan wasa ne na tarayya tsakanin maza da mata. Wato maza da mata duk na gudanar da wannan wasa. Kimanin mutane goma zuwa sama ne suke gudanar da shi. Wannan wasa ne na dandali, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Wasan na tafiya da waÆ™a, amma ba ya buÆ™atar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

    7.15.1 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa za su kasu kaso gida biyu, su riÆ™a fuskantar juna. Sannan za su riÆ™e hannunwan juna daga É“angarorin guda biyu. Daga nan kuma É—aya zai hau bisa hannuwan a kwance. Yaran za su riÆ™a rausaya wanda ke saman hannuwan nasu tare da yin waÆ™a kamar haka:

    O maciji,

    Zalala maciji,

    Ga maciji a bakin kogi zalam.

    Haka za su yi ta yi sai adadin da aka É—iba ya Æ™are. A nan wanda ke saman zai sauka/za ta sauka, wani/wata kuma ta/ya hau. Wannan wasa ne na nishaÉ—i da kuma motsa jiki.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.