Gidan Kurciya

    7.16 Gidan Kurciya

    Wannan wasa ne na tarayya tsakanin maza da mata. Wato maza da mata duk na gudanar da wannan wasa. Kimanin mutane ishirin zuwa sama ne suke gudanar da shi. Sai dai wasan ya fi daÉ—i idan aka samu yara da dama sun taru domin gudanar da shi. Akan rera waÆ™a cikin wannan wasa, amma ba a buÆ™atar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

    7.16.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali da kuma makarantun boko.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa da dare da kuma rana, lokacin wasanni a makarantu.

    7.16.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan yi da’ira, sannan su dafa kafaÉ—un juna. Wannan zai ba da damar a samu tazara a tsakankaninsu. Sunan waÉ—annan tazara gidan kurciya. Mai fara wasa zai/za ta riÆ™a shiga ta gidan kurciya É—aya bayan É—aya tare da yin waÆ™a, yayin da sauran masu wasa za su riÆ™a amsawa kamar haka:

    WaÆ™a: Gidan kurciya,

    Amshi: Shaya.

     

    WaÆ™a: Wanda ya É“ata,

    Amshi: Shaya.

     

    Waƙa: Zai sha duka,

    Amshi: Shaya.

     

    Waƙa: Har da muntsini,

    Amshi: Shaya.

    Haka abin zai ci gaba, duk lokacin da mai wasa ya/ta tsallake gida É—aya ba tare da ta/ya shiga ba, masu wasa za su É—ira masa dundu. Haka mai wasa zai/za ta ci gaba har sai ta/ya gama yin sa/ta. Daga nan kuma sai mai yi nagaba ya/ta karÉ“a.

    7.16.3 Tsokaci

    Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki tare da samar da nishaÉ—i ga yara. Sannan yana koyar da nitsuwa da kuma bin Æ™a’ida.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.