Waran Warash

    7.17 Waran Warash

    Wannan wasa ne na yara maza da mata ke gudanarwa. Amma a wasu lokutan, akan samu mata ma suna yi. Yawan masu gudanar da shi na iya farawa daga biyu zuwa sama da haka, har zuwa biyar. Wasa ne da ba ya É—auke da waÆ™a. Sannan ba a buÆ™atar kayan aiki yayin gudanar da shi.

    7.17.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a gida, musamman lokacin bukukuwa kamar bikin aure ko na haihuwa.

    ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma ko kuma da dare.

    7.17.2 Yadda Ake Wasa

    Kowanne daga cikin masu wasa zai É—auki suna; ko dai Jamilun ko Goron ko Goruba, ko Kash, ko Aminun. Daga nan za a fara wasa ta hanyar furta:

    “Waran warash!”

    Yayin da aka yi wannan furuci, kowa zai sanya yatsu a Æ™asa, yawan adadin da ya ga dama. ÆŠaya daga cikinsu zai Æ™irga yatsun É—aya É“ayan É—aya ta hanyar ambaton:

    Jamilun,

    Goron,

    Goruba,

    Kash,

    Aminun.

    Zai riÆ™a taÉ“a yatsa a daidai lokacin da yake furta É—aya daga cikin kalmomin. Haka zai bi kan yatsun masu wasa gaba É—aya. Duk sunan da aka ambata a yatsar Æ™arshe da masu wasa suka sanya, to wannan mai suna ya fita. Daga nan zai janye gefe ya zuba wa sauran masu wasa namujiya.

    Yayin da wani É—an wasa ya fita, waÉ—anda suka rage a ciki suna da damar canza suna domin É—aukar sunan wanda ya fitan. Misali idan goruba ne ya fita, wani wanda ke da suna kash na iya cewa ya koma goruba ta hanyar furta:

    “Na canza zuwa goruba.”

    Haka za a ci gaba da fita É—aya bayan É—aya, har kowa ya fita a rage mutum É—aya. Wannan da bai fita ba shi ne ya faÉ—i, saboda haka hukuncin nasa ya hau kansa. Wadda ya faÉ—i a wannan wasa sakamakon da ke hawa kansa shi ne ci. Tun farkon wasa akan Æ™iyasce‘yar ci nawa ne. Wanda za a ci zai haÉ—a tafukan hannuwansa, wato bayan hannuwan na waje. Wanda zai ci kuma zai riÆ™a dukan bayan hannuwan da tafin hannunsa (har sai ya yi yawan dukan cin da aka Æ™iyasce). Daga nan kuma wanda ake ci zai fara gociya. Wato zai yi Æ™oÆ™arin É—auke hannunsa yayin da aka kawo duka. Idan ya ci sa’angoce wa dukar da aka kawo, to ya tsira. Idan kuwa bai goce ba, haka za a yi ta dukansa, har sai lokacin da ya goce. Mai ci kuma zai yi ta Æ™oÆ™arin duka cikin gaggawa da yaudara yadda wanda ake ci ba zai iya goce wa dukan ba.

    7.17.3 Sakamakon Wasa

    Sakamakon wanda ya faÉ—i wannan wasa shi ne ci, tamkar dai yadda aka yi bayani a sama.

    7.17.4 Tsokaci

    Wannan wasa yana buÆ™atar lissafi da zurfafa tunani. Domin kowane É—an wasa zai riÆ™a karantar tunanin abokan wasansa. Zai yi tunanin yatsu nawa za su sanya, domin ya sanya daidai yadda shi ne zai fita. Sannan wasan yana koyar da juriya da zafin nama da kuma jarumta.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.