Za Ni Za Ni Ye

    7.18 Za  Ni  Za  Ni  Ye

    Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin aiwatar da shi. Yana da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale. Abin da ya bambanta wasannin biyu kawai shi ne irin waÆ™ar da ake yi a cikin kowanne. WaÆ™ar wasan Za Ni Za Ni Ye ta kasance kamar haka:

    Za ni za ni ye,

    Za ni Kadisau,

    Kadisan doki,

    Dokin kara,

    Kara na albasa,

    Albashi kwaÉ—i,

    Zuciyar damo,

    Na faÉ—a kudu,

    Na kuma na faÉ—a kudu,

    Duk wanda waÆ™ar ta faÉ—a kan Æ™afarsa, to zai cire wannan Æ™afa, tamkar dai a wasar Lakkuma-Lakkuma Lale.Sakamako da amfanin wannan wasa duk iri É—aya ne da na Lakkuma-Lakkuma Lale

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.