Na Diba

    7.2 Na ÆŠiba

    Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya a gudanar da shi. Kimanin mutane biyu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

    7.2.1 Wuri Da LokacinWasa

    i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko a cikin gida ko Æ™ofar gida, ko dai wani wuri da yara ke taruwa.

    ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wani lokaci akan yi shi da dare idan akwai wadataccen farin wata.

    7.2.2 Kayan Aiki

    i. Æ˜asa

    ii. Tsinke mai É—an tsayi

    7.2.3 Yadda Ake Wasa

    Akan tara Æ™asa daidai gwargwado, sai kuma a tsikara tsinke a tsakiyar Æ™asar. Tsinken zai kasance mai tsawo yadda zai ratsa Æ™asar ya iso har Æ™asa. Daga nan yara za su fara É—iban Æ™asar É—aya bayan É—aya. Duk wanda lokacin É—ibansa ya zo, zai riÆ™a É—iba tare da waÆ™a kamar haka:

    Na É—iba,

    Na kuma na É—iba,

    Na sake na É—iba,

    Ga ladana.

    Wannan na nuna cewa, mai É—iban Æ™asar zai É—iba ne sau huÉ—u. Haka za su ci gaba da É—iba É—aya bayan É—aya, kowa yana tara Æ™asar da ya É—iba a gabansa. Za su riÆ™a yi suna matuÆ™ar taka tsantsan da tsinken da aka tsikara a tsakiya domin kada ya faÉ—i. Za ta kai lokacin da zai zama ‘yar Æ™anÆ™anuwar Æ™asa ce take riÆ™e da tsinken. A wannan lokaci, yara za su riÆ™a É—ibar Æ™asar a hankali, sannan kaÉ—an-kaÉ—an. Duk wanda wannan tsinke ya faÉ—i a lokacin É—ibansa, to ya faÉ—i. Sannan shi za a daka.

    7.2.4 Sakamakon Wasa

    Sakamakon wanda ya faÉ—i a wannan wasa shi ne dala. Za a tara Æ™asa, sannan wanda za a daka ya É—ora tafin hannunsa a kai. Masu daka kuwa za su riÆ™a dunÆ™ule hannusu na dukan kan bayan hannun nasa. Wannan ya danganta da yawan dakan da suka Æ™ayyade za su yi.

    7.2.5 Tsokaci

    Wannan wasa na samar da nishaÉ—i ga yara. Sannan yana buÆ™atar nitsuwa da taka tsantsan yayin gudanar da shi.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.