Kumbukululu

    7.21 Kumbukululu

    Wannan wasa ne da yara maza da mata duka sukan gudanar da shi. Adadin yaran da ke gudanar da shi na kaiwa biyar zuwa sama da haka. A yayin gudanar da wasan, akan samu guda a matsayin kumbukululu da kuma sauran ‘yan wasa. Wannan wasan dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, lokacin farin wata. Wasan yana tafiya da waÆ™a, sannan yana buÆ™atar kayan aiki yayin gudanar da shi. Kayan aikin kuwa shi ne kallabi ko wani tsumma da za a yi amfani da shi wurin yin kumbu kululu.

    7.21.1 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan nemi É—ankwali ko wani tsumma su rufe wa É—aya daga cikinsu ido. Wannan rufe ido akan kira shi kumbukululu, haka ma yaro ko yarinyar da aka rufe wa idanun. Daga nan yara za su watse. Kumbu kululu kuwa za ta riÆ™a bi tana laluÉ“e da niyyar ta kama kuma ta yanka. Duk wanda kumbu kululu ta yanka, to shi/ita ce za ta zama kumbu kululu. Yara za su riÆ™a waÆ™a kamar haka:

    Kumbu kululu kumbu kululu,

    In kin ji hayaniya ana da yawa,

    In kin ji hayaniya akwai nama.

    Da zarar ta kai sura, duk yara sai su watse. Haka za ta yi ta fama har Allah Ya ba ta damar kama É—aya daga ciki.

    7.21.2 Tsokaci

    Wannan wasa ne na nishaÉ—i wanda kuma hanya ce ta motsa jiki ga yara.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.