Zuciyar Mai Tsumma

    7.22 Zuciyar Mai Tsumma 

    Wannan ma wasa ne daga cikin wasannin da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanarwa. Yana tafiya da waƙa, sannan ana buƙatar kayan aiki kafin gudanar da shi. Akan samu tsoffin kaya da suka yayyage wanda da su ne Mai Tsumma (ɗaya daga cikin masu wasa) zai/ za ta yi amfani da shi. Kimanin mutane uku biyar zuwa sama da haka ne suke gudanar da wasan. Kamar sauran wasannin tashe, an fi gudanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.

    7.22.1 Yadda Ake Wasa

    Kamar yadda aka bayyana a sama, yara za su nemi kaya marasa kyau. Waɗannan kaya ne ɗaya daga cikinsu zai sanya. Wanda ya sanya kayan akan kira shi da suna ‘Mai Tsumma.’ Sannan za a shafa masa bula ko baƙin tukunya ko wani abu mai kama da wannan a fuska. Da zarar komai ya kammala, sai kuma a ɗunguma wurin tashe.

    Yayin da aka isa wurin tashe, Mai Tsumma zai samu gefe guda ya tsaya, ya ɓata rai. Ba zai ce wa kowa komai ba. Amma duk wanda ya gan shi ya san ransa a ɓace yake matuƙa. Sauran yara kuwa za su fara waƙa. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Zuciyar mai tsumma,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Tumbuna yau salla,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Babu kayan salla,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Babu rigar salla,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Babu wandon salla,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Babu hular salla,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Zuciyar mai tsumma,

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Malam ka sani kuwa?

    Amshi: A kusa take.

     

    Bayarwa: Malama kin sani kuwa?

    Amshi: A kusa take.

    Wannan waƙa ta danganta da maza ne ke wasan ko mata. Idan aka lura waƙar da aka kawo a sama akan yi ta ne yayin da maza ne ke wasan. Kamar yadda aka yi ta ƙirgo kayan maza. Idan kuwa mata ke wannan wasa, za su riƙa ambaton kayan sawa na mata irin su; zane da ɗankwali da makamantansu.

    7.22.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan hannunka-mai-sanda ne ga iyaye. Yana nusar da iyaye da zaburar da su wurin ɗinka wa yara kayan salla. Kamar yadda rashin hakan kan jefa yaran cikin halin ƙunci da baƙin ciki. Sannan waƙar tana kundace wasu daga cikin kayan sawa ko dai na mata ko na maza da Bahaushe ke amfani da su.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.