Dakin Tsuntsu

    7.23 ÆŠakin Tsuntsu 

    Wannan wasa ne da yara maza da mata duka sukan gudanar da shi. Da wuya a furta adadin yaran da ke gudanar da wasan kai tsaye. Domin kuwa yaro ko yarinya guda É—aya na iya yin wasan. Wani lokaci kuwa yaran sukan kai goma ko ma sama da haka. Wani lokaci yara sukan rera Æ™aramar waÆ™a yayin wannan wasa. Iyaka kayan aiki da ake nema shi ne Æ™asa mai damshi. Shi ya sa aka fi gudanar da wannan wasa lokacin damina, yayin da Æ™asa ke da damshi. Sannan akan yi wannan wasa ne da hantsi ko da yamma. Yakan kasance kuma a cikin gida ko a Æ™ofar gida. Amma ba wasan dandali ba ne.

    7.23.1 Yadda Ake Wasa

    Kowanne daga cikin masu wasa zai kwarfaci Æ™asa ya tara a gabansa. Daga nan zai ajiye Æ™afarsa guda a Æ™asa, ko dai ta dama ko ta hagu. Sai ya yi amfani da wani É“angare na Æ™asar da ya tara ya lulluÉ“e Æ™afar. Zai sanya Æ™asa mai yawa domin ta kasance mai kauri bisa Æ™afar. Sannan zai daÉ“e Æ™asar da hannunsa ko da bayan takalmi silifa saboda ya yi Æ™arfi. Da zarar ya kammala, sai ya fara Æ™oÆ™arin zare Æ™afar a hankali. A wannan lokaci mai zarewa yakan yi waÆ™a kamar haka:

    ÆŠakin tsuntsu kar ka rushe,

    In ka rushe ba na son ka.

     

    ÆŠakin tsuntsu kar ka rushe,

    In ka rushe ka ci amana.

    Burin yaro shi ne ya tsare Æ™afarsa ba tare da Æ™asar ta ruguje ba. Idan ya ci nasarar zare Æ™afar daidai, gurbin da ya zare Æ™afar zai samar da abin da ake kira É—akin tsuntsu. Wannan shi ya kasance tamkar É—akin kwana ga wasan yara.

    Da zarar an kammala É—aki, sai kuma a fara gina katangar gida. Ita ma dai akan yi amfani da Æ™asa mai damshi ne a yi ta. Amma akan yi É—an tattara Æ™asa ne kawai a layi ba sai ta yi tudu sosai ba, a matsayin katanga.

    Haka za a ci gaba da wasa. Wani lokaci akan yi ‘yartsana da É“ararren kara, a sanya cikin wannan É—aki a matsayin masu gida. Yayin da aka gaji da wasa kuwa, za a baje waÉ—annan gidaje ne. Yawanci yara sukan ce:

    “A ci moro, a ci moro.”

    Sannan sai su baje É—akunan da hannuwa ko Æ™afafunsu.

    7.23.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaÉ—i ga yara. Sannan wasan kwaikwayo ne yaran suke yi. Misali idan aka yi la’akari da kwaikwayon tsarin ginin gidajen Hausawa da suke yi. Kusan kowanne daga cikin masu wasa yana gina irin gidansu ne, ko wani gida da ya taÉ“a gani.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.