Ticker

‘Yar Akuyata

7.28 ‘Yar Akuyata 

Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. Yana tafiya da waƙa. Sannan akan yi amfani da balo-balo yayin gudanar da shi. Wasan yakan iya kasancewa a cikin gida ko ƙofar gida ko dandali. Sannan ba dole sai an samu haɗakar yara kafin gudanar da shi ba. Babu kuma wani ƙayyadadden lokaci da aka ware na gudanar da wannan wasa. Yakan kasance da hantsi ko da yamma.

7.28.1 Yadda Ake Wasa

Mai wasa zai cika balo-balo da iska. Sai kuma ya kama bakin balo-balon da yatsu daga gefe da gefe. Zai riƙa jan bakin yadda zai na buɗewa kaɗan-kaɗan yadda iska za ta samu damar fita tare da wata ƙara (ɓii-ɓii). Zai riƙa yin hakan tare da waƙa. Ga yadda abin yake kasancewa:

Mai Wasa: ‘Yar akuyata,

Iskar Balo-Blo: Ɓii-ɓii

 

Mai Wasa: Za ki ci dusa?

Iskar Balo-Blo: Ɓii-ɓii

 

Mai Wasa: Wa ya hana ki?

Iskar Balo-Blo: Ɓii-ɓii

 

Mai Wasa: Inna da baba.

Iskar Balo-Blo: Ɓii-ɓii

A wannan gaɓa mai wasa zai sake balo-balo ɗin yadda iskar da ke ciki za ta fita da wata ƙara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments