‘Yar Cake

    7.30 ‘Yar  Cake 

    Wannan wasa da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. An fi gudanar da wasan da damina lokacin da ƙasa take da damshi. Sannan an fi yin sa cikin gida ko ƙofar gida. Ba ya tafiya da waƙa. Sai dai akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Kayan aikin kuwa shi ne kibiya ko wuƙa ko dai wani abu mai tsini.

    7.30.1 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan zana gidan dara a ƙasa, wuri mai damshi. Yawan gidan daran za su iya kaiwa goma ko makamancin haka. Daga nan mai wasa zai riƙe kibiya ko wuƙa ko wani abu mai tsini. Zai riƙa jefawa da ƙarfi yadda tsinin abin da ke riƙe hannunsa zai cake cikin gidan darar. Ƙa’idar wasan ita ce; mai wasa zai riƙa bin gidan darar ɗaya bayan ɗaya yana cakewa.

    Yayin da ya jefa sai kuma ba ta cake ba, ma’ana ta faɗi, to ya faɗi ke nan. Saboda haka, abokin wasansa zai karɓa. Haka ma idan ya jefa, sai ba ta shiga gidan darar da ya dace ta shiga ba, nan ma ya faɗi. Yayin da ya cake a dukkanin gidajen kuwa (ɗaya bayan ɗaya), zai sayi gida. Yadda ake sayan gida kuwa shi ne; zai ja layuka daga kusurwowi huɗu na gidan da zai saya. Daga wannan lokaci, idan ya zo ba zai tsallake wannan gida, ba sai ya cake a cikinsa ba.

    7.30.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana buƙatar nutsuwa da ƙwarewa. Yana kuma koya wa yara seti.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.