Ticker

Sigina Uku Danja

7.33 Sigina Uku Danja 

Wannan ma wasa ne na yara maza da mata, wanda kuma ke da zubi da tsari irin na wasan Sunkuya Dundu.Abin da ya bambanta su kawai shi ne, a sigina uku danja ba sai lokacin da mutum ya sunkuya ake dukansa ba. A maimakon haka, akan yi sigina ne guda uku da hannu. Yayin da aka yi ukun bai waigo ba, to za a ɗira masa duka. Yadda ake siginar kuwa shi ne, za a kulle yatsun hannu a buɗe, sigina ɗaya ke nan. Za a yi hakan har sau uku.

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


WASANNI A ƘASAR HAUSA7

Post a Comment

0 Comments