Ticker

6/recent/ticker-posts

Odi-Odi

7.36 Odi-Odi

Wannan wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. Yana tafiya da waƙa, amma ba a buƙatar kayan aiki domin gudanar da shi. Wasan na dandali ne, saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

7.36.1 Yadda Ake Wasa

Ɗaya daga cikin ɗan wasa na kasancewa kura, Kura ce ke kamu yayin wasa. Kura za ta rufe idanu wanda, sannan ta juya wa ‘yan wasa baya. ‘yan wasan kuwa za su fara neman wurin ɓuya. Daga nan kura za ta sanya waƙa, sauran ‘yan wasa na amsawa. Misali:

Kura: Odi-odi,

Amshi: O!

 

Kura: Matar malam,

Amshi: O!

 

Kura: Ta ci sakwara,

Amshi: O!

 

Kura: Shi ma malam,

Amshi: O!

 

Kura: Ya ci sakwara,

Amshi: O!

Kura: Kura ta zo ne?

Amshi: O!

 

Kura: Babba ko ƙarama?

Amshi: Babba.

 

Kura: Gani nan zuwa!

Da zarar an kawo wannan gaɓa, kura za ta bazama kan ‘yan wasa. Waɗanda suka riga suka ɓoye za su yi likimo. Waɗanda kuwa ba su ɓoye ba, za su yi ta gudu tare da kura. Yayin da kura ta kama ɗaya daga ciki. To shi zai zama kura. Saboda haka, za a sake wasa daga fari.

7.36.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Baya ga haka, wasan na sanya musu jarumta da dabarun tseratar da kai.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments