Ticker

6/recent/ticker-posts

Biyar Ko Goma

7.4 Biyar Ko Goma

Wannan ma wasa ne wanda yara maza da mata duk sukan gudanar da shi. Mutane biyu ne suke gudanar da wannan wasa a tsakaninsu.

7.4.1 Wuri Da Lokacin Wasa

An fi gudanar da wannan wasa a dandali, wato da dare lokacin farin wata.

7.4.2 Kayan Aiki

Ɓawon gyaɗa guda biyu

7.4.3 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su yi zane a ƙasa mai kusurwa huɗu. Misali:

 

Daga nan za a raba shi zuwa gida biyu. Kowanne daga cikin ‘yan wasan zai ɗauki gida guda. Sannan za a zana layuka daga iyaka zuwa iyaka a kowanne gida. Saboda haka, kowane gida zai kasance an raba shi zuwa kashi biyar ko sama da haka. Misali:

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Daga nan masu wasa za su riƙa sanya ɓawon gyaɗa guda biyu a hannunsu, su jijjiga su watsar a ƙasa. Yayin da ɓawon gyaɗar suka kife dukkansu. To mai wasa na da maki goma. Yayin da kuma suka buɗe duka, to mai wasa na da maki biyar. Idan kuwa ɗaya ya buɗe ɗaya ya rufe, to mai wasa ya faɗi.

Duk wanda ya ci maki, zai ja ƙananan layuka a tsattsaye daidai da maki da ya ci a cikin layukan da ke gidansa. Haka za a yi ta yi har sai gidan ɗaya daga cikin‘yan wasa ya cika taf da yadda ba wurin da za a iya zana wani layin. Idan haka ta faru, to ya yi nasara ke nan.

7.4.4 Tsokaci

Wannan wasan na samar da nishaɗi ga yara. Sai dai duk da cewa iyawa na amfani, sa’a na tasiri a kan wasan.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments