Lakkuma-Lakkuma Lale

     7.5 Lakkuma-Lakkuma Lale

    Wannan wasa ne na yara maza da mata da ake gudanarwa a zaune. Yara biyu ma za su iya gudanar da wannan wasa. Sai dai yawan masu wasan na iya kasancewa biyar ko sama da haka.

    7.5.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    Wannan wasa ne na dandali. Saboda haka, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin da akwai farin wata.

    7.5.2 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan zauna su mimmiÆ™e Æ™afafunsu. Daga nan É—aya daga cikinsu zai fara waÆ™a tare da taÉ“a guiwowinsu É—aya bayan É—aya. WaÆ™ar kuwa ita ce kamar haka:

    Lakkuma-lakkuma yaki are,

    Yaki are huwa dumbabe,

    Dumbabe huwa Makka be,

    Mukka be Madina be,

    Asa ale aleti,

    Ale tibil bileti,

    Guju-guju babban zakara,

    Na asshatunan danja,

    Wush! 

    Duk guiwar Æ™afar da wannan waÆ™a ta Æ™are a kanta, to Æ™afar ta fita. Saboda haka, mai Æ™afar zai naÉ—e wannan Æ™afa. Haka za a yi ta yi har sai kowa ya fita saura Æ™afar mutum É—aya. Daga nan za a ce ya zaÉ“a tsakanin sama ko Æ™asa. Yayin da ya zaÉ“a sai a yi wannan waÆ™ar tsakanin wurin da ya zaÉ“ar (sama ko Æ™asa) da kuma Æ™afar da ba ta fita ba. Idan aka yi sa’a Æ™afarsa ta fita, to ya dace. Idan kuwa ba ta fita ba (wato sama ta fita ko Æ™asa) to ya faÉ—i ke nan. Don haka shi za a ci.

    7.5.3 Sakamakon Wasa

    Wadda ya faÉ—i a wannan wasa sakamakon da ke hawa kansa shi ne ci. Tun farkon wasa akan Æ™iyasce ‘yar ci nawa ce. Wanda za a ci zai haÉ—a tafukan hannuwansa, wato bayan hannuwan na waje. Wanda zai ci kuma zai riÆ™a dukan bayan hannuwan da tafin hannunsa (har sai ya yi yawan dukan cin da aka Æ™iyasce). Daga nan kuma wanda ake ci zai fara gociya. Wato zai yi Æ™oÆ™ari É—auke hannunsa yayin da aka kawo duka. Idan ya ci sa’ ar gocewa dukan da aka kawo, to ya tsira. Idan kuwa bai goce ba, haka za a yi ta dukansa, har sai lokacin da ya goce. Mai ci kuma zai yi ta Æ™oÆ™arin duka cikin gaggawa da yaudara yadda wanda ake ci ba zai iya gocewa dukan ba. 

    7.5.4 Tsokaci

    Wannan wasa ne da ke buÆ™atar jarumta. Duk wanda ya faÉ—i zai fuskanci ci. Dole ne ya kasance mai juriya yayin da ake dukan hannuwansa don gudun dariya da zolayar abokan wasansa. Sannan wasan na koyar da Æ™warewa kamar yadda mai ci zai ta Æ™oÆ™arin samun hannunuwan wanda yake duka a daidai. Wanda ake ci kuma zai yi ta Æ™oÆ™arin gocewa.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.