7.8 Talili Tali Yambo
Wannan ma wasa ne da yara maza da mata suka yi tarayya wurin gudanar da shi. Yana ɗaya daga cikin rukunnen wasannin zaune da ke da waƙa. Kimanin yara huɗu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Wani lokacin yawansu na iya kaiwa goma, ko ma sama da haka.
7.8.1 Wuri Da LokacinWasa
An fi gudanar da wannan wasa a dandali, da dare, musamman lokacin farin wata.
7.8.2 Yadda Ake Wasa
Yara na zama a tsarin da’ira. Amma sukan kasance kusa-kusa da juna. Sai kuma kowanne yaro ya ɗora ƙafarsa ta dama (idan wasan ‘yar dama ce) a cinyar wanda ke zaune gefe da shi. Idan kuwa wasan ‘yar hagun ce, to kowane yaro zai ɗora ƙafarsa ta hagu kan cinyar wanda ke zaune hagu da shi. Haka abin zai kasance wato an zagayo.
Da zaran an kamala ɗora ƙafa, za kuma a fara waƙa. Mutum ɗaya ko biyu ne za su riƙa ba da waƙa, saura kuwa na amsawa. Wanda ya fara ba da waƙar zai doki ƙafar da ke kan cinyarsa. Wanda aka doki ƙafar tasa shi ma zai doki ƙafar da ke kan cinyarsa. Haka abin zai yi ta tafiya. Wato dai kowa na dukan ƙafar da ke bisa cinyarsa, amma ɗaya bayan ɗaya. Sai dai dukan yakan kasance daidai gwargwado ne, ba mai zafi sosai ba. Amma duk da haka, yaran da ke da ƙarancin juriya har kuka sukan yi.
7.8.3 Waƙar Wasan Talili Tali Yambo
Bayarwa: Talili tali yambo,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Ɗan wasanmu na bara,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Bana ma ya dawo,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Yayinsa ake yi,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Kowa ya doki kansa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Kowa ya doke ni sannu,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Ni ko na doke shi sosai,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Kowa ya ceci kansa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Mu ga wanda bai iyawa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Allah kashe makoɗa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Gero ya samu kansa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Allah kashe makoɗa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Dawa ta samu kanta,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Allah kashe makoɗa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Maiwa ta samu kanta,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Allah kashe makoɗa,
Amshi: Talili!
Bayarwa: Wake ya samu kansa,
Amshi: Talili!
Za a yi ta jero sunayen abinci da ake shukawa, har sai adadin waɗanda mai waƙar ya sani sun ƙare.
7.8.4 Tsokaci
Wannan wasa yana koya juriya ga yara. Wanda bai jure ba yayin wasan har kuka yakan/takan yi. Sannan wasan na ƙara wa yara sani game da nau’ukan abincin da Bahaushe ke shukawa.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.