Girjim

    8.1 Girjim

    Wannan wani wasa ne dangin dara. Sau da dama akan yi caca da shi. Wato a sanya kuɗi kan cewa duk wanda ya yi nasara a wasan, to zai mallake kuɗin. Wani lokaci akan sanya wani abu daban da ba kuɗi ba, kamar tufafi da makamantansu. Maza manya ne suka fi gudanar da wannan wasa. Sai dai akan samu wasu lokuta da yara ke yi, musamman waɗanda suka gani daga manya. Mutane biyu ne suke gudanar da shi, sai dai za su iya fin yawan haka yayin da aka yi taron dangi.

    8.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan gudar da wannan wasa a filayen caca, da keɓaɓɓun wurare cikin kasuwanni. Yara sukan yi a gindin inuwoyin bishiyoyi a cikin unguwanni.

    ii. Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko rana ko ma da yamma. Sai dai ba a faye yin sa da dare ba.

    8.1.2 Kayan Aiki

    i. Ƙodagon goruba ko taura ko ƙwallon mangwaro ko duwatsu ko makamantansu.

    8.1.3 Yadda Ake Wasa

    Akan zana gidajen dara talatin da shida (36) ko a yi ‘yan gurabu yawan wannan adadi. Akan yi gidajen darar shida a tsaye, shida kuma a kwance, jere da juna reras. Daga nan kowa daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa zai zaɓi nau’in‘ya’yan da zai yi amfani da su (ko dai tsinke ko dutse ko ƙwallon mangwaro ko na taura ko ƙwadagon goruba da makamantansu). Kowa zai ɗauki ‘ya’ya goma sha biyu ya zuba su ta hanyar jerewa a layuka biyu na farko da ke gabansa. A wani lokaci akan yi taron dangi, wato mutane biyu ko sama da haka su kasance suna tafiya da tare. Wato su yi shawara kafin ɗayansu ya yi tafiya. Wani lokaci kuma za a samu wani mutum da ba ya cikin wasa amma yana sanya baki a wasan. A irin haka, abokin wasan wanda ake sa wa baki zai iya ƙin yarda, musamman idan wasan ba na sa baki  ba ne.

    Daga nan mai tafiyar farko zai fara tafiya ta hanyar tura ɗa zuwa gidan da ke gaba da shi. Za su ci gaba da tafi karɓa-karɓa. Akan tura ɗa zuwa gidan gaba ko baya ko gefe. Yayin da ‘ya’ya biyu na ‘yan wasa daban-daban suka mannu da juna, mai tafiya zai cinye wannan ɗa da ke jikin ɗansa (idan akwai gidan da zai iya sauka a bayan ɗan). Idan kuwa mai wasa ya kai ga shi ga ɗaya daga cikin gidaje biyu da ke kusurwa a gaban abokin karawarsa, to ya shiga sarki. Saboda haka za a naɗa shi sarki ta hanyar ƙara ɗa ɗaya a kan wannan ɗa da ya shiga sarki da shi. Sarki yana da fawar doguwar tafiya. Saboda haka zai iya cin ɗa da ke nesa da shi. Amma sarki ba zai iya cin sarki daga nesa ba. Ɗa kuwa ba zai iya cin sarki ba, ko da suna kusa da juna, sai dai idan ya rage ɗa ɗaya ne kacal ga mai wasa.

    Wasu lokuta mai wasa kan ambaci: “girjim” daidai lokacin da ya ɗaga ɗa daga wani gida zuwa wani gida, musamman domin zolaya. Hakan na faruwa yayin da ya shanshani ƙamshin nasara kan abokin karawarsa, wato domin zolaya. Yayin da aka cinye‘ya’ya mai wasa ko aka kulle shi gaba ɗaya, to an kore shi ke nan.

    8.1.4 Wasu Daga Cikin Dokokin Wasa

    Duk da akan samu bambance-bambancen dokokin wasan daga wuri zuwa wuri, an yi ƙoƙarin kalato wasa guda daga cikinsu kamar haka:

    i. Sanya baki a wasan da ba ya sa baki laifi ne.

    ii. Idan ɗan wasa bai ya samu damar ci sai bai ci ba a wasan da take sizin, to za a ɗauke wannan ɗan da ya ƙi ci da shi.

    iii. Yayin da mai wasa ya dace ya ɗauki sizing sai ya yi wata tafiya daban, to sizin ɗin ya huce.

    iv. Duk wanda aka shiga ɗaya daga cikin kusurwoyin gabansa biyu, dole ya naɗa wa abokin wasansa sarki.

    v. Sarki yana fawar doguwar tafiya.

    vi. Ɗa ba ya iya cin sarki sai ya kasance shi kaɗai ne ya saura a garin mai wasa.

    vii. Sarki zai iya cin ɗa daga nesa.

    viii. Sarki ba zai iya cin sarki daga nesa ba.

    8.1.5 Tsokaci

    Wannan wasa yana kaifafa tunani kasancewar sai an zurfafa tunani tare da yin lissafi yayin gudanar da wasa.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.