Macukule

    8.7 Macukule

    Wannan wasan tashe ne na maza manya. Adadin masu gudanar da shi na iya kaiwa biyar ko sama da haka. Sannan akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Domin kuwa akan samu É—aya daga cikin masu wasa ya yi shigar Gwari. Sannan ya shafe fuskarsa da farar Æ™asa ko wani abu mai kama da wannan. Zai kuma riÆ™e Æ™warangwal na kan wata dabba, kamar akuya ko tinkiya da makamantansu. Kamar dai sauran wasannin tashe, an fi guduanar da shi da dare, bayan an sha ruwa.

    8.7.1 Yadda Ake Wasa

    ÆŠaya daga cikin masu wasa zai yi shigar Gwari, kamar dai yadda aka bayyana a sama Æ™arÆ™ashin 6.7. Sai kuma su É—unguma wurin tashe. Da yake manya ne kuma maza, sukan bi dandali ne wurin sana’o’i da kuma wuraren da mutane ke zama. Yayin da suka zo wurin da za su yi tashe, wanda ya yi shigar gwari zai juya murya, ya riÆ™a magana irin ta gwarawa. Zai riÆ™a ba da waÆ™a sauran kuwa na amsawa. Ga yadda waÆ™ar take:

    Bayarwa: Salamu’alaikum, ga baÆ™onku Nagwari,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Shekara ta dawo,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Ni ma na dawo.

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Allah Ya kawo,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Zan muku tashen Gwari,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Yaro ba zai iya ba,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Ni ma da Æ™yar na koya,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: A can Æ™asarmu Gwari,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Kan kare da daÉ—i,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Romon kan jaki daÉ—i,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Tun ba wurin idon ba,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Tsutsa shinkafa ce,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Tana ko taliya ce,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Kan Æ™uda kuÉ“ewa,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Majina kitse ce,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: TumbuÉ—i da daÉ—i,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Alhaji namu yana nan,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Ba Alhajin tsiya ba,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Ya sha ruwa lafiya lau,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Wani Alhaji na nan,

    Amshi: Macukule.

     

    Bayarwa: Bai sha da lafiya ba,

    Amshi: Macukule.

    8.7.2 Tsokaci

    HaÆ™iÆ™a wannan wasa yana samar da nishaÉ—i musamman ga masu kallo. Idan mutum ya dubi yadda mai waÆ™ar ya taÆ™arÆ™are yana maganar Gwari, dole abin ya ba shi sha’awa da dariya. Sannan wasan na nuna cewa, al’adun al’ummu sun bambanta da juna. Haka abin yake duk da ma an gina waÆ™ar wasan ne kan raha da kuma ban dariya. Kuma fa da ganin kan jaki, romonsa zai yi daÉ—i.

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.