Cite this article as: Lawal, G. (2023). Ƙaikayin Zuci: Juyayi Da Nuna Tausayi A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 210-213. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.025.
Ƙaikayin Zuci: Juyayi Da Nuna Tausayi A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)
NA
Garba LAWAL
Email:
garbalawal195@gmail.com
08032787160/09137303797
Tsakure
Wannan takarda ta ƙunshi tsokaci ne ko
bayani kan yadda Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya sarrafa wasu zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci a
waoƙoƙinsa domin nuna
tausayi da juyayin faruwar wasu abubuwa marasa daɗin ji, da suka faru
ga wasu mutane. Wato dai duk batutuwan da hankalinsu yake bayyanawa a waƙoƙin suna da alaƙa da ban tausayi ko
juyayi da alhinin faruwarsu. Ya sarrafa ire-iren waɗannan zantuttuka ne
sakamakon yadda batututuwan suke sosa masa zuciya a duk lokacin da ya tuna da
faruwarsu. Sa’annan kuma sukan sanya masa ɓacin rai da damuwa a
duk lokacin da tuna da su Har wa yau kuma mawaƙin ya yi amfani da waɗannan zantuttuka ne a
waƙoƙinsa domin nuna
tausayi ga mutanen da ibtila’in ya faɗa musu
Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi,
Tausayi, Juyayi, Ƙaiƙayin Zuci
Gabatarwa
Waƙa zance ne mai tsari
da yake tafiya cikin hikima da basira wanda wasu mutane masu fasaha da balaga
da azanci suke aiwatarwa cikin sautin murya mai zaƙi da jan hankali.
sa’annan kuma a isar da wasu muhimman saƙonni da za su amfanar
da jama’a wajen ganin sun gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum. Wato dai mawaƙa wasu mutane ne da
Allah (SWT) ya hore masu wata baiwa ta hikiimar iya sarrafa wasu zantuttuka ko
kalmomi cikin waƙa da nufin faɗakarwa ko ilmantarwa ko wa’azantarwa ga
jama’a. A fanen ilimi akan nazarci ire-iren waɗannan waƙoƙi ne domin a fito da
wasu muhimman abubuwa masu amfani da ke iya taimakawa wajen inganta rayuwar
al’umma. Mafiya yawa daga cikin mutane masu sauraron waƙa sun fi mayar da
hankalinsu ne ga daɗin kiɗan da aka haɗa da waƙa ko kuma zaƙin muryar mawaƙi. Wato babu ruwansu
da saƙonnin dake ƙunshe a cikin waƙar. Saboda haka, manufar
wannan takarda ita ce tsokaci kan wasu waƙoƙi da Aminu Ladan
Abubakar (ALA) ya rera a inda ya sarrafa wasu zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci
masu nuna tausayi da juyayi kan abubuwan da suka faru ga wasu mutane. Mawaƙin ya yi amfani da
zantuttuka da kalmomi mabambanta domin nuna damuwa da alhini da juyayi dangane
da faruwar wasu abubuwan takaici da suka faru ga wasu mutane.
Taƙaitaccen Tarihin
Aminu Ladan Abubakar (ALA)
Masana da manazarta
irin su Imran (2008) da Umar (2011) da Hamza (2011) da Isa (2013) da Muhammad
(2014) da Yakasai da Sani (2021) DA Sani &
Suleiman (2022). duk sun yi tarayya a kan cewa an haifi Aminu Ladan Abubakar
(ALA) a ranar Talata 2 ga watan 10 shekara ta 1973 cikin shekarar hijira ta
1394 a Unguwar Yakasai, Ƙaramar Hukumar Birni da kewayen Jihar Kano. Sai dai kuma
an yaye shi a wata unguwa ta daban, wato a unguwar Ƙofar Wambai a hannun
kakanninsa. Daga baya sai iyayensa suka yi ƙaura zuwa ƙaramar Hukumar
Nasarawa inda suka zauna a unguwar Tudun Murtala.
Aminu Ladan Abubakar
(ALA) ya fara karatu da koyon karatun addini a ƙarƙashin Malam Muhammad
Sani wanda ake yi wa laƙabi da Malam Ɗan-Sakkwato wanda a
wurinsa ne ya haddace izifi biyar daga cikin Alƙur’ani mai Girma.
Baya ga nan kuma ya yi karatu a wata makarantar Islamiyya mai suna Zaharaddeeni
Islamiyya ta Tudun Murtala ƙarƙashin kulawar Malam
Usman Tudun Wada, inda ya fara tun daga rabin aji har zuwa aji shida, wanda
daga baya kuma ya zama ɗaya daga cikin alaman
makarantar.
Aminu Ladan Abubakar
(ALA) ya fara karatun boko a wata makarantar Firamare mai suna Tudun Murtala
Primary School, inda ya yi karatu a tsakanin shekarar 1980 zuwa 1986. Daga nan
kuma sai ya halarci makarantar Sakandare ta Dakata Kawaji wato (Government Senior
Secondary School, Dakata Kawaji), daga shekara ta 1986 zuwa 1992. Bayan ya
kammala karatunsa na sakandire a shekara ta 1992, sai ya dakatar da ci gaba da
karatun sakamakon matsaloli na rayuwar yau da kullum har tsawon shekaru goma
sha biyu (12). Daga baya ya koma makarantar gaba da sakandare a shekara ta 2000
inda ya shiga makarantar fasaha ta Kano wato (School of Technology, Kano) inda
ya yi karatu a fannin zane-zane wato (Department of Arts and Industrial Design)
a wannan makaranta, ya samu shedar difiloma ta ƙasa a shekarar (2003).
Sosuwar Zuci Mai Nuna
Tausayi
Zantuttuka ko kalmomi
masu jiɓi da sosuwar zuci
masu nuna tausayi kan zo ne sakamakon jin kai ko nuna damuwa game da faruwar
wani abu maras kyau ga wani mutum ko wata al’umma. Mawaƙa kan yi amfani da
ire-iren waɗannan zantuttuka ko
kalmomi domin nuna tausayinsu ga wani abin takaici da ya faru ga wata al’umma
ko wani mutum. Wato dai kamar yadda Aminu Abubakar (ALA) ya nuna tausayinsa ga
al’ummar Arewacin Nijeriya dangane da rashin haziƙin shugaba kuma
jagora wanda waɗansu marasa imani
suka yi masa kisan gilla saboda ƙabilanci da ɓangaranci, kamar dai
yadda mawaƙin yake bayyanawa a cikin waƙarsa inda yake cewa:
Jagora: Ya
jama’ar Arewa!
Ga
ta’aziyyar Sardauna,
Shi
da firaministansa,
Abubakar
da Sardauna,
Sun
tafi ba magandansu,
Yanzu
muna cikin ƙuna,
Ba
makwafi na halinsu,
Ga
shi Arewa sai kuka.
‘Y/Amshi: Gamji
maza abin koyi,
Ahmadu
Bello Sardauna,
In
na tuno wafatinsa,
Sai
ya saka ni in kuka,
Jagora:Ni
abin da ka ban tausai,
Nai
marinafin idanuna,
Ƙwalla na tuttuɗo guna,
Tay
yo gare kumatuna,
Sardauna
bai magaji ba,
Ko
da ka ji da Sardauna,
Amma
iyakaci su na.
(Waƙar Gamji Maza)
Waɗannan baituka da suka
gabata daga wannan waƙa ƙunshe suke da zantuka masu jiɓi da sosuwar zuci
masu nuna tausayawa da takaici da nuna damuwa na irin wannan babban rashin da
mutanen Arewa suka yi. Mawaƙin ya nuna tausayawarsa na rashin
magajin Sardauna a ɓangaren halin ƙwarai da jarunta,
inda ya ce ko da ka ji ana kiran wani da Sardauna to iyakacinsa suna amma babu
hali irin na Sardauna.
Har wa yau kuma mawaƙin ya ci gaba da
sarrafa ire-iren waɗannan zantuttuka da
kalmomi masu jiɓi da sosuwar zuci
domin nuna tausayawarsa ga al’ummar Arewa, inda yake cewa:
Jagora:Daga
kashe su Sardauna,
Anka
yi decreen ƙarya,
Sun
ka yi thirty four decree,
Dokoki
na hamayya,
Anka
rugurguje aikin,
Amadu
babu alkunya,
Northern
sation policy,
Anka
baje su ba ƙarya.
‘Y/Amshi:
Jagora:An
izini a ƙasar Hausa,
Hausa
ta zam harshen aiki,
Daga
kashe su Sardauna,
Anka
baje wannan aiki,
Wani
abu na ban haushi,
Sanda
akai kisan haƙƙi,
Sai
Ibo sun ka hau fati,
Sun kashe
Gamji Hamshaƙi.
‘Y/Amshi:Hawayena
suna ta zuba,
Ga
juyayin gudun hijira.
Haƙiƙa duk waɗannan zantuttuka ne
da ke nuna tausayi da juyayi na abubuwan da suka faru ga al’ummar Arewa na
rashin gwarzon shugaba wanda kuma a dalilin hakan aka rugurguje duk wasu
tsare-tsare na ci gaba da ya kawo wa al’ummar Arewacin Nijeriya. Saboda a
dalilin rashinsa aka wargaje tsarin yin amfani da harshen Hausa a duk wata
mu’amala da ta shafi harkokin gwamnati, wato dai wannan wata Hasara ce babba ga
al’ummar Arewa na rashin yin amfani da harshen Hausa a harkokin gwamnati da ma
sauran al’amura da suka shafi rayuwar yau da kullum. Saboda haka, lallai wannan
abin tausayi ne da juyayi ga duk wata al’umma da ta tsinci kanta a irin wannan
yanayi, ba ma al’ummar Arewacin Nijeriya kaɗai ba.
Sosuwar Zuci Domin
Nuna Juyayi
Zantuttuka ko kalmomi
masu nuna juyayi ko alhini kan samu ne sakamakon faruwar wasu lamurra marasa daɗin ji da suka faru a
baya ga wasu mutane fitattu ko wata al’umma da sauran su. Akan nuna juyayi ko
alhini ne ga wani lamari da ya faru wanda ka iya tayar da hankali ko kawo firgici
ko sanya damuwa a zukatan al’umma. Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya nuna juyayinsa
da alhini ga al’ummar garin Maiduguri da maƙwabta, mawaƙin ya bayyana
batutuwa da dama waɗanda ya ji ko ya gani
da idonsa game da lamarin rikicin, wanda ya sanya wasu mazauna garin yin hijira
domin tsira da rayukansu da dukiyoyinsu. Kamar dai yadda yake ambatawa a waƙarsa inda yake cewa:
Jagora:Ina
zaune na hangi mutum,
Da matatai
suna ta bara,
Da
hange nai alamu nai fa,
Babu
kama da masu bara,
Da
‘yan ‘ya’ya maza, mata,
A
gunsu da dama masu jira,
Alamomi
na mai gajiya,
A
tare da su suna ta bara,
Da
sun ka iso gare ni,
Na
tambaye shi ya ce “gudun hijira.”
Amshi:Hawayena
suna ta zuba,
Ga juyayin
gudun hijira.
Jagora:Ya
ce mani “By Profession,”
A
aiki na fi fo hijira,
Ya ce
mani “malami ne ni,
Na
koyarwa a gwanin fiira,
Ya
ce mani ga iyalaina,
Waɗanda da su mukai
hijira,
Amaryata
da yaranta,
Babu
amonsu ko nai kira,
Suna
mace, ko suna raye,
Allah
masani Sarkin ƙudura
Duk waɗannan baituka da suka
gabata na daga ƙunshe suke da zantuttuka ko bayanai masu jiɓi da sosuwar zuci
masu nuna juyayi da alhini ga wani bawan Allah da ya tsinci kansa daga cikin
masu gudun hijira a sanadiyyar yaƙe-yaƙen boko haram da ya
faru a garin Maiduguri.
Mawaƙin ya nuna juyayi da
alhininsa game da yadda wasu suka yi gudun hijira daga garin Maiduguri zuwa ƙasashen maƙwabta domin samun tserewa.
Wato dai yadda yake nuna tausayi da juyayi ko alhini ga mutanen da abin ya
shafa, musamman ga waɗanda suka yi gudun
hijira suka baro gidajensu da dukiyoyinsu da iyalansu da sauran ‘yan uwa. Wasu
kuma suka baro sana’o’insu suka koma mabarata sakamakon gudun hijira a
sanadiyyar rashin kwanciyar hankali da ke faruwa a garuruwansu. Haƙiƙa duk waɗannan batutuwa da
mawaƙin ya zayyano a waƙar, abubuwa ne na ban
tausayi da sanya juyayi ko alhini ga duk wanda hakan ta faru gare shi. Aminu
Ladan Abubakar (ALA) ya ci gaba da nuna alhininsa da juyayi ko tausayawa ga
wani magidanci da ya tsinci kansa a cikin masu gudun hijira kamar dai yadda
yake cewa:
Jagora:Ya ce mani
kalli ‘ya’yana,
Ƙanana ne mukai hijira,
Manya a cikinsu mata
ne,
Na bar su gida na zo
ni bara,
Idan da akwai sukuni,
In yi gadi sai na ɗau ƙadara,
Wurinmu abin mu kai
baki,
Mu bauta ciraku mai ƙuduri,
Ko ɗan aiki, ko ko aike,
Ko dai masinja mai
shara.
Jagora:Nan take
jiki ya ɗau rawa,
Na kasa tsayi na kasa
zama
Cikin sa’a a motata,
Ina da tufa ta
alfarma,
Na ba su tufa, na ba su
kuɗi,
Ya karɓa kau yana kyarma,
Ya sake fasa mani
kuka,
Na jin daɗi da alfarma,
Na rarrashe su, sunka
tafi
Na
kasa tsayi, na kasa zama (Waƙar Juyayi).
Tabbas waɗannan baituka da suka
gabata ƙunshe suke da zantuttuka masu jiɓi da sosuwar zuci, waɗanda ke nuna tausayi
da alhini. Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya bayyana yadda zantawarsu ta kasance a
tsakaninsa da wani bawan Allah wanda ya tsinci kansa a yanayin gudun hijira.
Mawaƙin ya nuna kaɗuwarsa matuƙa na ganin yadda
wannan bawan Allah da iyalansa, ga ‘yan yara ƙanana a cikin yanayi
na ƙasƙanci, tare da yawon
bara domin samun abin da za su sanya a bakin salati. Sa’annan kuma akwai
‘ya’yansa mata manya wanda bai san halin da suke ciki ba. Shi dai buƙatarsa ya samu wani
aikin yi kamar gadi ko masinja ko share-share ko ɗan aike da sauransu. Duk da cewa
mutumin babban malami ne a garinsu amma a sanadiyyar gudun hijira ya zama ƙasƙantacce. Waɗannan batutuwa sun
tayar da hankalin mawaƙin matuƙa da har ta kai ga na sosa masa
zuciya, musamman ma a duk lokacin da ya tuna da abin a cikin ransa.
Haƙiƙa waɗannan abubuwan da
mawaƙin ya bayyanaw a waƙarsa, wasu batutuwa
ne da suke nuna tausayi ko juyayi ga bayin Allah da suka tsinci kansu a yanayi
na gudun hijira. musamman ma ga wannan bawan Allah da mawaƙin ya samu zantawa da
shi a yanayi na ƙasƙanci sanadiyyar gudun hijira da ya tsinci kansa a ciki.
Kammalawa
An nazarci waɗannan waƙoƙi ne domin yin
tsokaci game da yadda Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya sarrafa wasu zantuka ko
kalmomi masu jiɓi da sosuwar zuci a
waƙoƙinsa. Mawaƙin ya sarrafa
ire-iren waɗannan zantuttuka da
kalmomi domin nuna tausayi da juyayi na wasu abubuwa marasa daɗin ji da takaici da
suka faru ga al’umma mazauna rewacin Nijeriya. Sai kuma yadda ya nuna yadda
wasu bayin Allah suka tsinci kansu a yanayi na gudun hijira. Haƙiƙa mawaƙin ya yi amfani da
fasaharsa ta waƙa wajen nuna tausayi da alhini ga waɗannan lamura da suka
faru. Saboda haka, ya yi amfani da wannan hanya wajen bayyana abubuwan da suka
sosa masa rai game da al’ummar Arewa wato dai ya bayyana abubuwan da suke cikin
zuciyarsa da nufin zaburar da al’ummar arewacin Nijeriya da su farka daga barci
domin kare mutunci da ‘yancin Arewa tare da ƙoƙarin zaburar da
manyan yankin Arewa wajen farfaɗo da martaba da mutuncin Arewa. Wato dai waƙoƙi ne da aka rera
domin nuna juyayi da alhini tare da tausayin yadda wasu abubuwa marasa kyau
suka faru ga wasu mutane da al’ummar wani yanki.
Manazarta
1. Barista, M.L. (2011).
Waƙoƙin Aminu Ladan
Abubakar ALA. Kano: Iya Ruwa Publishers.
2. Bashir, R. (2021).
Hotoncin Zuci A Waƙoƙin Baka Na Hausa: Tsokaci A Kan Wasu Waƙoƙin Maza Da Na Fada.
Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu
Bello.
3. Daniel, G. (1995).
Emotion Intelligence. London: Bantom Books.
4. Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa:
Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
5. Izard, C.E. (1977).
Human Emotion. New York: Plenum.
6. Lawal, G. (2022).
Sosuwar Zuci A Waƙoƙin Hausa Na Zamani: Nazari A Wasu Waƙoƙin Aminu Ladan
Abubakar (ALA). Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zariya:
Jami’ar Ahmadu Bello.
7. Sani, A-U. &
Suleiman, M. (2022). Tsattsafin Haliya: Wani Ɗigo Cikin Tafashen
Aminu Ladan Abubakar (ALA). In South Asian Research Journal of Arts, Language
and Literature, Vol. 4, Issue 2, Pp 77-77. DOI:
www.doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.005.
8. Satatima, G.I.
(2009). Waƙoƙin Ɗarsashin Zuciya Na Makaɗan Husa. Kundin Digiri na Uku. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe. Kano: Jami’ar Bayero.
9. Yakasai, S.A. da Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Amal Printing Press.
10. Yusuf, B. (2017).
Zuciya A Tunanin Bahaushe: Nazari Daga Waƙar Baka. Kundin
Digirin Farko, Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.