Alhamdulillah! Malan Tijjani LABARINA da my Dear, my Lover, my Sweet Heart, matata ke nan. Labarin dogo ne.
Wato na gama
KAWAJI 86. Matata ta gama GGC DALA 88 muka fara soyayya kamar wasa 88 zuwa 89 a
kayi mana aure.
Na gajarce maka
labari matata ko yaji balantana barkono bata ta6a yi ba, amma ka san yau da
kullum sai ALLAH. Muna 6atawa amma da kanmu muke shiryawa.
Har yanzu idan
muna zolayar juna da wasanni kai ka ce aurenmu na zumunci ne. Shiɗinma
irin na ɗan mace da ɗan namiji.
Kuma yadda
muke wasanni da barkwanci ko a gaban 'ya'yanmu balantana abokai da 'yan uwa sai
haka.
Idan na ce zan ara
aure wAllahi Malan Tijjani a kullum kalmarta ita ce ALLAH Ya kawo ta gari sai
nace amin, idan ran maza ya 6aci kenan.
Ka san har yanzu
tana ce da ni my Sweety. ABBA shi ne sunan da ta canja min kuma daga dangina
har nata dangin kai mahaifiyarta ma Abba ne sunana a wajensu.
Mun haifi yara
goma (10) uku (3) sun rasu a ciki yanzu muna da Bakwai (7) 5 maza 2 mata. Muna
zaune a Happy Marrued Life country...
At least
shekarunmu nawa kenan Malan Tijjani? Mun yi oari kuwa? AlhamdulilLaah. Na gode.
Ni:
Kun lura ba a ce
Hide My ID ba ko? 😀 Saboda abin alkhairi suka shuka ba abin
kunya ba.
Daga Taskar
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +234 806 706 2960
A Kiyayi Haƙƙin Mallaka
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.