Ba Girin-Girin Ba Tai Mai

    Ba Girin-Girin Ba Tai Mai

    Wallaahi na dad'e ina wannan tunanin Malam. Ai don kar mutum ya yi magana ne a ce da shi hwuen hwuen 😄 shi ya sa muke yin shiru. 

    Ina da laburare cike da litattafai a k'ark'ashin matattakalan hawa bene na da ma ofishina har da ofishin gida amma da yawa ban karanta su ba. Malam kar wasu su ji labari.

    Amma da yawa masu ik'irarin karanta litattafai suna 'ba'batun yin hakan ba don wata k'aruwa suke karantun litattafan ba sai don kawai su k'irga yawan litattafan a shekara guda. 

    Don ai ance amfanin ilimi aiki da shi ko? In ka karanta littafi me ka tsinta na ilimi a ciki? In ka gano wani abu a littafin me ka yi da shi na k'aruwar kai ko ka k'ari al'uma da shi? 

    Ko kawai karanta littafi kake ko kike yi in kun gama ku d'auko wani ku karanta sannan ku d'auko wani shi ma ku karanta da anyi magana ku ce kun karanta litattafai dubu?

    In aka dubi makaranta litattafan sai a ga babu wata shaidar ilimin da mutum ya samu yana tasiri a rayuwarsu? Illa kawai dai surutun ana karatun.

    Jama'a mu dinga k'ank'an da kanmu wajen nuna mu masu ilimi ne ko masu yawan karatu ne. Don duk karatun mutum idan ba ya amfani da ilimin to hutun jaki yake da kaya.

    Kar kuma ku manta salon d'aukar ilimi ya soma canjawa. Yanzu ba a tara ilimi don k'ure sanin juna ko nuna fifikon malanta. 

    Dalili? Google!

    Daga Taskar

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +234 806 706 2960

    A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.