𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum wa rahmatullah. Malam na dade da aure amma bamu samu haihuwa ba. Matata
tana yi mun biyayya sosai bani da wata matsala tare da ita. Kwatsam sai soyayya
ta shiga tsakanina da 'yar gidan Kanin babana, ta yarda zata aureni amma bisa
sharadin cewa idan na aureta sai na saki matata ta gida. Duk da cewa yarinya ce
mai ilimin addini, nayi ƙoƙarin fahimtar da ita cewa wannan sharadin bai dace ba, amma taƙi
amincewa wai dole sai nace na yarda da haka. Amma fa iyayenmu duk ba su san da
wannan sharadin ba. Nace mata eh na yarda, amma acikin zuciyata ban amince ba.
Kuma tabbas ina sonta amma bazan iya sakin Uwargidana saboda ita ba. Duk da
cewa akwai yiwuwar ita ɗin
zan samu haihuwa da ita In shã Allahu. (Duk dangin mamanta suna da yawan
haihuwa) Yanzu haka anyi mana baiko, saura 'yan kwanaki a daura mana aure. Nace
Shin Malam mene ne halascin auren nan namu? Domin ni dai gaskiya bazan saki
matata ba..
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Lallai wannan
alkawarin ko sharaɗin
da kuka Ƙulla
ba halastacce ba ne, don haka bai lazimceka ka cika sharaɗin ba. Amma dai aurenku da
matarka ta farko yana nan, babu abin da ya taɓashi.
Haka nan aurenka da amarya ma ya yiwu mutukar dai an Ƙullashi bisa sharudan da
musulunci ya ajiye.
Duk wani sharaɗin da ya kunshi saɓon Allah, ko umurni da
mummunan abu, bai lazimci musulmi mumini ya cikashi ba.
Abu na biyu
kuma ina yi maka wasiyyah tare da ni kaina da kuma dukkan mazajen aure cewa
muji tsoron Allah wajen mu'amala tsakanin iyalanmu bisa adalci da kyautatawa.
Kada soyayyar wata daga cikinsu ya sanya ka wulakanta wata. Kuma kada ka munana
wa wata don burge wata.
Allah ne ya
sanyasu a ƙarƙashin
kulawarmu bisa amana kamar yadda Alƙur'ani da Sunnah suka karantar. Kuma
Allah ya sanya mu sutura ne garesu kamar yadda suma sutura ne garemu.
Allah ya ce "SU
SUNA DA HAKKI (AKANKU KU MAZAJE) KWATANKWACIN WANDA KE KANSU".
Duk sanda
mutum ya nufi yin Ƙarin aure, zai fi kyau ya kokarta wajen kwantar da hankalin
matarsa ta gida tare da wa'azantar da ita a kan muhimmancin haƙuri.
Sannan kada ka yiwa amaryarka irin wannan alkawarin na zalunci. Allah shi
kiyayemu.
Ita dai
haihuwa Allah ke bayarwa. Idan kayi haƙuri ita ma Uwargidan zata haihu in Allah
yaso. Kai dai ka rokeshi ya baka masu albarka shike nan.
WALLAHU
A'ALAM.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.