Babi Na Shida: Wasannin Yara Mata

    Wasannin Yara Mata

    6.0 Shimfiɗa

    Wannan babi yana ɗauke da wasannin yara mata daban-daban. Ya haɗa da masu ƙarancin shekaru da matsakaita da kuma ‘yan mata. Sannan ya ƙunshi dukkanin rukunonin wasannin mata, kamar tashe da wasannin dandali; ko dai na tsaye ko na zaune ko na guje-guje. An rattabo waɗannan wasanni ne ba tare da keɓe su rukuni-rukuni ba. Dalilin hakan kuwa shi ne, kasancewar an rigaya an kawo bayani game da rabe-raben wasanni cikin babukan da suka gabata. Wato dai, babban burin wannan babi shi ne rattabo wasannin mata da kuma yadda ake yin su, tare da waƙoƙinsu (ga waɗanda ke da shi da kuma kayan aiki/ga waɗanda ke da shi).

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8. 


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.