Ticker

6/recent/ticker-posts

BABI NA UKU - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 96)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

WAƘOƘIN AIKACE-AIKACE

3.0 Gabatarwa

A babin da ya gabata, an yi bayani ne tare da ba da misalan waƙoƙin Hausawa na gargajiya da suka shafi wasannin yara maza da mata na dandali da kuma wasannin tashe na yara maza da mata. Wannan rukuni kuwa zai karkata ne zuwa ga misalan waƙoƙin gargajiya na Hausawa da suka shafi wasu ɓangarori ko al’amuran rayuwar Bahaushe, musamman aikace-aikace. Wannan kuwa ya ƙunshi waƙoƙin da ake rerawa yayin gudanar da ayyuka daban-daban da suka haɗa da daɓe da daka da kuma niƙa da makamantansu. Sai dai za a kawo waƙoƙin ne kawai ba tare da nazartar su ba. ke nan akwai buƙatar nazarin waƙoƙin ɗaya bayan ɗaya domin fito da falsafar da kowacce waƙa ta ƙunsa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments