Bitar Ka'idojin Rubutun Hausa a Wadansu Kagaggun Labarai

    Cite this article as: Zarewa, U.S. & Adamu, S. (2023). Bitar Ƙa'idojin Rubutun Hausa a Waɗansu Ƙagaggun Labarai. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 176-180. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.020.

    Bitar Ƙa'idojin Rubutun Hausa a Waɗansu Ƙagaggun Labarai

    Umar Sunusi Zarewa
    School of Secondary Education Languages
    F.C.E (Tech.) Gombe
    08032702586
    umarzsanusi@gmail.com

     Da 

     Sani Adamu
    Department of Languages and Cultures, 
    Federal University, Gusau, Zamfara, Nigeria
    Phone Number: 07065411971
    Gmail: adamufsk3501@gmail.com

    Tsakure

    Wannan aiki ya mayar da hankali ne a kan ƙa'idojin rubutun Hausa. Haka kuma ya bayar da muhimmanci ƙwarai a kan irin katoɓarar da wasu marubuta ke tafkawa a fagen amfani da ƙa'idojin rubutu musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa. A yayin gudanar da wannan aiki, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da: Bitar ayyukan da suka gabata, karance-karancen litattafan ƙagaggun labarai da kuma taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun Hausa. Wannan binciken ya gano cewa ba a fagen amfani da ƙa'idojin rubutun Hausa kaɗai ba, marubutan sukan samu matsala ƙwarai musamman a wajen ginin jimla. Wannan aiki ya tabbatar da cewa duk waɗannan kurakuran ana samun su ne sakamakon mafi yawancin marubutan suna da ƙarancin ilimi a kan lamarin da ya shafi ƙa'idojin rubutu. A bisa haka ne wannan muƙalar ke ba da shawarar cewa, marubuta su yi ƙoƙari wajen inganta iliminsu, musamman a fagen amfani da ƙa'idojin rubutu domin hakan zai taimaka wa masu karatu wajen samun sauƙin fahimtar saƙonnin da ke cikin littattafansu.

    Fitilun Kalmomi: Ƙa’idojin Rubutu, Zube, Rubutu, Marubuta

    1.0 Gabatarwa

    Alamomin rubutu na nufin ‘yan ɗigagga da zane-zane da ake amfani da su yayin da ake rubutu. Ƙa'idojin rubutu kuwa waɗansu dokoki ne ko ladubba da aka gindaya da ya kamata mai rubutu ya kiyaye wajen rubutunsa (Bunza, 2002:16).

    Masana da dama, na gida da na waje sun yi aiki tuƙuru wajen daidaita rubutun Hausa ta hanyar amfani da ƙa'idojin da suka dace. Masana kamar su: (Lepsius, 1862) da (J.F. Schon da Prietzer, 1902) da (Mischlich, 1906) da (Westerman, 1911) duk sun gudanar da ayyuka daban-daban dangane da ƙa'idojin rubutun Hausa. Haka kuma an gudanar da taruka daban-daban domin gyara ƙa'idojin rubutun Hausa tun daga shekarar (1912) har zuwa (1980).

    Duk da irin wannan ƙoƙarin da masana suka yi bai hana samuwar kura-kurai a cikin rubutu ba musamman a cikin littattafan ƙagaggun labaran Hausa, domin mafi yawan masu rubuta su ilminsu ba mai zurfi ba ne. Za a tarar da masu aiwatar da rubuce-rubucen ba su zarce takardar kammala firamre da sakandare ba. Idan kuma aka sami matakin ilminsu ya zarce na sakandare, ba Hausa suka karanta ba asali. Idan kuma har yanzu Hausar suka karanta, ba su fahimce ta ba sosai

    Wannan muƙalar ta dubi irin kurakuran da masu rubutu cikin harshen Hausa ke tafkawa a yayin da suke rubutu, musamman a cikin litattafan ƙagaggun labarai. Haka kuma za ta mayar da hankali wajen fito da wasu daga cikin ƙa'idojin rubutun Hausa tare da bayar da ƙananan misalai a kan yadda ya dace a yi amfani da su a cikin litattafan.

    1.1 Ra'in Bincike

    An ɗora wannan binciken ne a kan ra'in ƙwaƙƙwafi (Close reading). An ɗora wannan aikin bisa wannan ra'i ne sakamakon bin diddigin da aka yi wa wasu litattafan ƙagaggun labarai na Hausa domin fito da kura-kuran marubuta a cikin littattafan. Ra'in ƙwaƙƙwafi shi ne da ke nazarin rubutu ta ɓangaren amfani da kalmomi da jimloli da kuma ma'ana a cikin rubutu. Ra'in yana nazarin abin da aka rubuta da kuma yadda aka rubuta shi kamar yadda Snow, da Connor, (2016) suka ruwaito.

    1.2 Dabarun Bincike

    Domin samar wa wannan bincike ingantaccen muhalli, an yi amfani da gogaggun hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da:

    a. Bitar ayyukan da suka gabata

    b. Karance-karancen wasu littattafan ƙagaggun labarai

    c.Taƙaitaccen nazari a kan ƙa'idojin rubutun Hausa

    d. Bincike ta hanyar amfani da yanar gizo

    2.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Rubutu Da Ƙa'idojinsa

    Rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo da ake amfani da shi a tsakanin al'umma. Wannan kuwa ya samo asali tun lokacin da al'ummar idanun al’ummar Hausawa suka buɗe dangane da harakar rubutu a faɗin duniya. Rubutu na ɗaya daga cikin hanyoyin da al'ummar Hausawa ke isar da saƙonninta musamman ta hanyar wallafa litattafai, jaridu da mujallu, da dai sauransu.

    Dangane da ma'anar rubutu kuwa, masana da dama sun ba da gudummuwa sosai. A bayanin Pavert (1993:8) cewa ya yi "Rubutu wata dabara ce ta yin wasu alamomi da za su wakilci magana". Shi kuwa Yahya (1988:1) ya bayyana cewa "Rubutu na nufin yin amfani da zayyana wasu alamomi a kan takarda ko a kan wani abu mai bagire don sadar da magana".

    2.1 Ƙa'idojin Rubutu

    Ƙa'idojin rubutu na nufin dokoki ko ladubba da ya kamata mai rubutu ya kiyaye a lokacin da yake rubutunsa. Waɗannan ƙa'idoji ne ke gyara rubutu da sanya masa tsarin da zai ba da dammar ya karantu (Sa'id, B. 2004). Wasu daga cikin waɗannan ƙa'idoji sun haɗa da:

    1. Ƙa'idojin raba kalma

    2. Ƙa'idojin haɗe kalma

    3. Nuna mallaka

    4. Alamomin rubutu

    Waɗannan rukunnai da aka lissafa a sama su ne ke ƙunshe da dokokin rabawa da haɗe kalmomi a yayin da ake rubutu. Misali, kalmomin korau, dirka, tsayayyen wakilin suna da dai sauransu. Haka kuma suna ɗauke da kalmomin doguwa da gajeruwar mallaka. Sannan kuma suna ɗauke da dokokin da ke bayani a kan yadda ake amfani da manya da ƙananan baƙaƙe a lokacin da ake rubutu. Haka kuma suna ɗauke da alamomin rubutu. Wasu daga cikin waɗannan alamomi sun haɗa da:

    A. Ayar tsayawa/alamar tsayi (.)

    B. Waƙafi (,)

    C. Waƙafi mai ruwa (;)

    D. Alamar tambaya (?)

    E. Alamar motsin rai (!)

    F. Ruwa biyu (:)

    G. Alamar zancen wani (" ")

    H. Alamar zarce (...)

    I. Karan ɗori (-)

    J. Baka biyu ( ( ) ).

    3.0 Waiwaye A Kan Ma'anar Ƙagaggen Labari

    Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar ƙagaggen labari. Misali: (Yahaya 2016:2) Cewa ya yi "Ƙagaggen labari, labari ne da ke cike da zantukan hira da nishaɗantarwa wanda ba da gaske ya taɓa faruwa ba”. Yahaya (1988:7) Ya bayyana tarihin rubuce-rubuce na ƙagaggun litattafai bai daɗe sosai ba, domin kuwa an same su ne bayan shigowar Turawa masu yaɗa addinin kirista. Turawa kamar irin su J.F Schon (1957) da sauransu.

    3.Kura-kurai A Cikin rubutun Hausa

    Ko shakka babu akan sami kura-kurai da dama a cikin rubutu wanda hakan ba ƙaramin cikas yake haifarwa a wajen fito da ma'anar saƙo ba. Irin waɗanann kura-kuran akan same su a wajen ƙirar kalmomi, ginin jimla da kuma sauran wuraren da ke da alaƙa da dokokin rubutu. Yanzu ga waɗansu misalai na jimloli da za a iya dubawa kamar haka:

    1. Aminu bai je makaranta ba.

    2. Wanda bai ji bari ba, ya ji hoho!

    3. Wane ne ya zo?

    4. Matarsa malama ce.

    5. Waccan akuyar tawa ce.

    6. A bar shi ya je karatu.

    7. Wannan al'ummar (Hausawa) suna da karimci.

    8. An yi mini wasa da hankali.

    9. Alhaji ya wuce buguzum-buguzum.

    10. Kayan da aka sarrafa ga su kamar haka:

    Idan aka yi la'akari da waɗannan misalan da aka lissafa a sama za a ga cewar, ƙa'idojin rubutu sun taka muhimmiyar rawa wajen fito da ma'anar waɗannan jimloli. Idan da kuwa za a cire waɗannan ƙa'idojin to da rubutun na iya hargitsewa ta yanda ma'anar ma za ta iya canzawa.

    Ta wani ɓangare kuma za a iya kawo misalai na wasu jimloli da rashin amfani da ƙa'ida kan iya haifar da sauyawar ma'ana ko kuma ya sanya jimlolin su zama masu harshen damo. Misali:

    1a. Ba shi ya ci (Let him eat/give him to eat/allow him to eat)

    1b. Bashi ya ci (He was credited)

    2a. Yaƙi ya je (He went for a war)

    2b. Ya ƙi ya je (He refuse to go)

    3a. Kin tafi kin bar ni ? (Quetion)

    3b. Kin tafi kin bar ni. (Comment)

    A nan ma idan aka duba za a ga ƙa'idojin rubutu sun yi aiki sosai wanda idan da za a cire su mai karatu ba zai samu fahimtar abin da ake nufi ba sosai.

    3.2 Nazarin Kura-Kurai A Wasu Litattafan Ƙagaggun Labarai Na Hausa

    Ko shakka babu littattafan ƙagaggun labarai na Hausa na cike da ɗumbin kura-kurai wanda har ya sa ake ganin wannan a matsayin gazawar marubuta littattafan ƙagaggun labaran. Samuwar irin waɗannan kura-kuran kan juya akalar saƙon da marubuci ke ƙoƙarin isarwa zuwa wata kafa/kusurwa ta daban. Ga dai misali a cikin wasu littattafai:

    a. Fateema ta ce kusan kullum abinda ke faruwa a gidanmu ke nan kullum sai ya daketa yace sai ta auri ɗan 'yar uwarsa, ita kuma ta dage bazata aure sa ba (Ribar biyayya, 2021:1)

    A cikin wannan zancen za mu ga cewa ba a yi amfani da alamomin kyautata rubutu ba. Ya kamata a yi amfani da alamar zancen wani. Haka kuma akwai wurare da yawa da ya kamata a sanya alamar tsayawa (aya), amma ba a sanya ba. Sannan rubutun sam ba a yi amfani da dokokin rabawa da haɗewa ba a cikinsa. Ga wasu misalan kamar haka:

    b. Tace yauwa gogo saisa nake sonki mema zakiyi dashi bani ina miki komi ba barima nai miki shara sai kiban kudin iloka (Matar Soja, 2022: 2)

    A wannan misalin da ya gabata za a ga cewar, marubucin wannan littafin ya tafka kura-kurai masu dama a cikin rubutunsa, domin kuwa rashin amfani da ƙa'ida ya janyo sauyawar ma'anar wasu kalmomi kamar: "Saisa", Bani" da kuma "Barima" waɗanda duk kalmomi ne da ke zaman kansu kuma suna ɗauke da ma'ana ta daban a cikin rubutun Hausa. Ga wasu misalan kamar haka:

    c. In ma ta yi mezanyi da ita tacigaba da masifa inbaka santa meyasa baka saketaba yace baze yihuba yarinyar kanen daddy ce fa (Rainon ta zan yi, 2014: 23)

    A wannan misalin ma za a ga cewa bayan cakuɗe rubutun da aka yi ta hanyar rashin yin amfani da dokokin raba kalma, an kuma haifar da sauyin ma'ana wajen rubuta jimlar "Yiwu ba" wadda marubucin ya rubuta kamar haka: "Yihuba".Ga wasu misalan kamar haka:

    d. Wayarta dake gefene yafara ringing dasauri tasa hannu tadau wayar hade dasawa a kunne tana fadin my one and only umma kin wune lafiya? daka dayan bangaren umma tace muneera kizu gida muna da bukatar ganinki akwai magana mai muhimmanci dazamuyi tana karasa fadan haka ta kashe wayar (Zaman Hostel, 2022: 1-2)

    e. Yayan mahaifinta wanda ake kira da baba bello shiya kalle muneera yace, muneera inaso kibude kunnowanki da kyau sanan kuma ki saurareni da kunnen basira, inason kisan ciwa abunda muka zaba miki a rayuwa har abada bazai taba zama cutarwa a garekiba saidai yazama alheri, kallonshi takeyi cikin rudo domin bata fahimce inda ya dosa ba (Zaman Hostel, 2022:3)

    f. "Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowanne ɗan'Adam da irin tasa ƙaddarar, na wani yafi na wani amma sam kai baka ɗauki kaddara ba" (A Gidanmu Take, 2020:1). A cikin wannan misali da ya gabata za a ga samuwar kura-kurai da dama waɗanda da za a yi amfani da dokoki to da ana sa ran rubutun ya kasance kamar haka:

    Haba Ahmad! Me ya sa ba za ka ɗauki ƙaddara ba? Ka sani fa kowane ɗan Adam da irin tasa ƙaddarar. Sai dai ta wani ta fi ta wani, amma kai sam ba ka ɗauki kaddara ba.

    g. Aiko zaki amayar da kayan cikin kine (Babban gida, 2015: 2)

    A waɗannan misalan da suka gabata na 'e' da 'f' sai dai a ce Allah ya kyauta! domin kure da gazawar da aka samu a cikin rubutun har ya wuce misali. Idan aka lura da kyau za a fahimci cewa mafi yawan kalmomi da jimlolin da aka yi amfani da su a cikin rubutun an saɓa ƙa'ida sosai. Waɗannan kura-kurai duk suna faruwa ne sakamakon gazawar marubutan wajen tashi tsaye domin neman ilimin da zai ba su damar inganta rubutunsu. Ga wasu ƙarin misalai kamar haka:

    h. ashraf yabiya tare da sa hannu cikin aljihu ya ciro 'yan dari biyar guda shida sababbi (Shu'umin namiji, 2019: 2)

    A wajen rubutun Hausa, kuskure ne a yi amfani da ƙaramin baƙi wajen rubuta sunan yanka kamar yadda waɗannan marubuta suka yi. A doka ana fara rubuta sunan yanka da babban baƙi. Haka kuma a misalin da ya gabata na "h" an samu kuskure a wajen rubuta kalamar "Aiko" da "Zaki" waɗanda kalmomi ne masu cin gashin kansu a Hausa.

    Sanannen abu ne cewa a rubutun Hausa ba a liƙa wa kalmomin dirka kowacce irin kalma walau a gaba ko a baya. Duk inda kalmomin dirka suke suna fitowa ne su kaɗai. A waɗansu lokutan akan sami masu rubutu su rinƙa rubuta su a cikin litattafansu kamar haka:

    i. Alhaji ya ce " Ba ita bace waccance "

    j. Menene haka Alhaji? (Maraicin Nawara, 2020: 17)

    Idan aka lura za a ga cewar duk an haɗe kalmomin na dirka wato "Ne" da "Ce" wanda kuma hakan kuskure ne.

    A wasu jimlolin kuwa akan sami wasu marubuta masu amfani da kalmomin dirka a muhallin/wurin da ba su dace ba. Wato sai su rinƙa sanya dirka jinsin namiji a muhallin da ya kamata a sanya ta mace. Misali:

    k. Ga ta fara, ga idanu, idan ka gan ta sai ka ce Balarabiya ne (Shu'umin namiji, 2019: 8)

    l. Nan take sai Amina ta tuna cewa wannan ai irin motar Usman ne (Shu'umin namiji, 2019:8)

    m. A bayan ɗakinsa ce ta ɓuya, wannan ne ya sa har Kadija ta fita ba ta gan ta ba (Shu'umin namiji, 2019: 19)

    Idan aka lura da waɗannan misalan za a ga cewa an samu kura-kurai na sanya kalmomin dirka a muhallin da bai dace ba. Kuma hakan kuskure ne a cikin rubutu.

    Alamar hamza waƙafi ne da ake sanyawa a saman gaɓar kalma (Ba a ƙasa ba) domin rabawa a tsakanin gaɓar da ta ƙare da wasali da kuma maƙwaɓciyarta da ta fara da wasali (Ba a amfani da wannan alamar a farkon kalmar da ta fara da wasali) Ana amfani da wannan alama ne saboda dalili biyu: Na farko domin nuna cewa ba ɗaurin wasali ko tsawon wasali ake nunawa ba. Na biyu kuwa, sauƙaƙa furuci, (Bunza, 2001:184-186 ). Misali: Mu'amala, sa'a, ,ɗabi'a,fara'a,Sa'adiyya, da dai sauransu.

    Marubuta ba su cika amfani da wannan alamar hamza ba, hakan ya sanya suke sanya ta a inda bai dace ba. Misali:

    n. Da Magajiya da Ummi Aisha suka dinga had'ata a dole ta hak'ura Ihsan ta karb'a (Ummi Aisha, 2019: 35).

    A cikin wannan misalin za a ga marubucin bai yi amfani da alamar hamza a kan yadda ya dace ba domin kuwa bai sanya ta a muhallinta ba.

    o. Daria sukai dukkansu suka nufa wajen mai adaidaitasahun akai ciniki (Ummi Aisha, 2019: 35). Bayan kwamacalar da wannan marubucin ya tafka, kuma za a ga cewar a rubutun nasa ya yi amfani da kalmar "Daria" wadda sam ba kalmar Hausa ba ce.

    4.0 Sakamakon Bincike

    Sakamakon wannan binciken ya yi daidai da hasashen binciken. Tun daga taken wannan aikin za a fahimci cewa ana da niyyar bayyana gazawar marubuta litattafan ƙagaggun labarai na Hausa ta fuskar rashin amfani da ƙa'idojin rubutu yadda ya dace. A nan za a iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin kuwa ko da aka duba wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labaran, sai ga shi an samu kura-kurai masu tarin yawa wanda har aka kawo misalan kaɗan daga cikinsu. Kura-kurai da ake samu a cikin rubutu suna da tasiri ƙwarai wajen daƙushe daraja da ƙimar marubuta. Baya ga wannan matsala kuma, har ila yau suna janyo sauyawar rubutu ta fuskoki da dama kamar haka:

    1- Ta fuskar ma'ana

    2- Ta fannin ginin jimla

    3- Ta fannin ƙirar kalma

    4- Amfani da wasu haruffa da babu su a harshen Hausa. Misali, "x".

    Waɗannan matsaloli da aka kawo a sama suna da tasiri sosai wajen janyo wa marubuta litattafan ƙagaggun labarai na Hausa wasu abubuwa kamar haka:

    1- Durƙushewar kasuwa.

    2- Gazawa wajen cimma manufa.

    3- Gundurar da masu karatu.

    4- Rikitar da masu karatu wajen ƙoƙarin fahimtar saƙo.

    5- Cin amanar ilimi.

    6- Lalata darajar harshen Hausa da kuma sauran abubuwa makamantan waɗannan.

    7- Amfani da kalmomin da ba na Hausa ba a matsayin na Hausa.

    Wannan ba abin mamaki ba ne, domin kuwa bincike ya nuna cewa mafi yawa daga cikin marubuta litattafan ba su da ƙwarewa sosai ta fannin ilimin da ya shafi ƙa'idojin rubutun Hausa da ma Hausar baki ɗaya. Haka kuma ba su tuntuɓar masana a yayin da suka gudanar da rubutunsu domin a yi musu gyara. Suna ganin kowane gauta ja ne, wanda kuma bah aka abin yake ba.

    4.1 Kammalawa

    A cikin bayanan da suka gabata na wannan muƙalar, an yi ƙoƙarin fitowa da ma'anar rubutu da ƙa'idojinsa. Haka kuma an yi gajeran sharhi dangane da kura-kurai a cikin rubutun Hausa inda har aka bayar da wasu ‘yan misalai. Bayan wannan kuma, an yi ƙoƙarin fito da wata ma'ana daga cikin ma'anonin ƙagaggen labari. Sannan kuma an bayar da misalai da dama dangane da kura-kurai waɗanda aka zaƙulo a cikin wasu daga cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa. A cikin wannan aiki da aka gabatar za a ga cewar, kura-kurai a cikin litattafan ƙagaggun labarai na Hausa abu ne wanda ya kamata marubuta su kiyaye, domin ta hanyar kiyayewar ne za su samu damar isar da saƙonninsu cikin sauƙi kamar yadda wannan muƙalar ta yi bayani.

    Manazarta

    1.       Adamu, A. (2017). Maraicin Nawara. First Class Writters Assocition Com.L.T.D. Kano

    2.       Abdullahi, A. (2022). Nana Fatima. Interligent Writters Association Com.L.T.D. Kano

    3.       Aliyu, S.R (2020). Ummi Aisha. Writters Forum Company Press Limited Kaduna Zariya

    4.       Abdulmajid, R. (2014). Rainonta zan yi. Khairat-up Company press limited Kaduna Zariya.

    5.       Bunza, A.M (2002). Rubutun Hausa (Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa) Don Masu Koyo Da Koyarwa. Lagos State, Nigeria.

    6.       Inuwa, Y.F. (2021). Ƙa'idojin rubutun Hausa. Gwammaja printing press, Nigeria Limited, Kano state.

    7.       Junaid, A. (2020). Ribar biyayya. Interligent writters Association com.L.T.D.

    8.       Muhammad, A. (2022). Matar Soja. Writters Association Company, press Kano.

    9.       Tukur, S. (2022). Farar Wuta. Writters association Company Press Limited Kano.

    10.    Yahaya, I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M Da 'Yar'aduwa T.M. (2007). Darussan Hausa, Domin

    11.    Yahaya, S. (2019). Shu'umin Namiji. Hajara Love Company Press Limited Kano

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.