Salam. Barkanmu da yin hidimar babbar sallar shekarar 2023. Allah Ya maimaita ma na.
A ran Asabar, 24/6/2023 mun yi taron tunawa da Alhaji, Dr. Mamman Shata, cewa an yi ma sa addu'a ta cika shekaru 24 da rasuwa, a PLBC, watau ofishin Dr. Muttaka Rabe Darma (Turmin Dakan Zinari wanda ba'a ba da aron sa) A wurin taron, an tattauna cewa a sarakunan Arewa ma su wukar yanka kaf, ba wanda Shata bai je masarautarsa ba ya wake sai mutum daya, shi ne Shehun Borno mai rasuwa.
Toh, na so in ba da amsa amma sai Allah Ya mantar da ni ban ce komi ba, alhali, na yi niyyar bayar da amsa.
Toh, in dai Dodo ne, na Bilkin Sambo, na Izzatu-mai-benen-bene, amma, benen duk na waka, ya taba yi ma Shehun Borno waka, a lokacin ya na hakimci a Kukawa. An yi taro a wani wuri ana buki, ga maroka sun cika wurin. Sai Alhaji Shata ya lura maroka sun addabi shi hakimi. Sai Shatan ya kada baki ya ce ma sa:
'Ranka ya dade, kai fa za ka zama Shehun Borno nan da watanni idan wannan Shehun na yanzu ya kau, don haka ga doka na kafa ma, kada ka kara zuwa a irin wannan wurin inda maroka za su mayar da kai kamar kowa don ba al'adar gidan Sarautar ku ba ne, a ce ana ganin Shehun Borno na fama da mutane a wurin buki, kuma ma bukin, wanda bai kasaita ba'
Wuf, sai hankalinsa ya karkato ga Shata, ya ce : 'Kai, Shata, da gaske ka ke? Akwai fa maza a gabana wadanda su ka zama manya a gwamnati, ni, ba ni ma sa rai'
Sai Dodo ya ce ma sa: Toh wallahi ka sanya rai, kai Allah za Ya bai wa Sarautar Shehun Borno'
Wakar da ya yi ma sa a wurin ita ce mai amshin'Hakananne Mamman Kanen Idi Wan Yalwa'
Da Allah Ya hukumta ya zama Shehun Borno sai ya aiko ma Shata, ya tafi can ya yi wargi, nan ma sai ya yi ma sa waka, mai salon amshin dai na Hakananne Mamman Kanen Idi Wan Yalwa.
Wanda ya ba ni wanga labarin shi ne Alhaji Shehu Tsatso Katsina wanda ya zama sankiran Dodo na lokaci mai tsawo. Ya shaida ma ni cewa da shi Shata ya je Kukawa, don haka a gabansa Shatan ya fadi waccan magana. Sannan, da shi aka je Borno nadin Shehu. Da ma su ka isa, Shehu ya yi dariya, ya ce ma Shata, 'ni ban yarda ba, ban da waka, akwai wasu baiwawwaki na musamman da Allah Ya ba ka'
Mun zanta da Shehu Tsatso a cikin Maris, 2000. Allah Ya gafarta ma su, Allah Ya gafarta ma na.
A wurin taronmu na PLBC, wanda ya tado wanga zance shi ne Alhaji Dikko (mai sunan Sarki) Bala Kofar Sauri. Shi ma, Haji Dikko, mu na yi ma sa godiya da wannan lura da kuma matashiya da ya yi.
Sai mu dora wannan batu a maysayin goron sallah babba ga masoya Cif Kwamanda na mawaka.
Daga Taskar
Malam Aliyu Kankara Ibrahim,
Wakilin Tarihin Sarkin Pauwan Katsina kuma mawallafin littafin tarihin Shata,
Asabar, 1/7/2023
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.