Dattijo Alhaji Nuhu

    Dattijo Alhaji Nuhu

    Dattijo Alhaji Nuhu ke nan wanda mahaifansa daga  Kano suka tafi wannan Kasar ta Burkina Faso fiye da  shekaru 200 da suka wuce, a Ouagadougou aka haife shi. Attajiri ne  daga harkar noman kayan marmari na lambu(Orchard) wanda ta hanyar  ne ya mallaki Æ™addarori masu yawan gaske a Æ™asar musamman gidaje da filaye. Ya baiwa al'ummar Hausawa da sauran Kabilu Musulmai da ba 'yan Æ™asar ba wani makeken fili a Zango dake Birnin Ouagadougou kyauta suka gina Masallacin Juma'a. A lokacin da Marigayi Thomas Sankara ya yi juyin mulkin da ya zamo sanadiyar zaman shi Shugaban Ƙasar, ya soma gyara fasalin tsarin Birnin Ouagadougou sai wannan Masallacin ya faÉ—o cikin wuraren da za a rushe. Al'ummar da suka mallaki wannan Masallacin suka yi mashi ke Æ™orafi akai sai ya naÉ—a kwamitin da zai gano silar samuwar wannan wuri idan ba ta haramtattar dukiya ne aka samar dashi  ba ya yi masu alÆ™awalin ba zai rushe shi ba, za a zaud'a daga gefen shi. Sanin silar dukiyar Alhaji Nuhu ne sanadiyar tsirar Masallacin(2017 ne na ziyarci Æ™asar)

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.