Daudun Bara

    Ni Daudun bara É—an Galadiman bara,

    Na saba bara ba na kwana ban ci ba,

    Kun ga rawar tuwo kun ga tattaken miya,

    Kun dafa kudaku abin cika mummuƙe,

    Kak ka ci kak ka sha rabon wani ba naka ba.

    Idan naka ne kana É—aka aka ba ka shi.

    Kura ta ga É—an bara É—an almajiri,

    Bari in bi ka É—an bara in shawo gari.

    Tahiya da taki ba ta zama É—ai da É—ai,

    Ni roÆ™o ni kai ga mata ‘yan arziki,

    Ke ƙwace ki kai ga mata ba su ba ki ba.

    Mai babban rabo ba zai wuce aljanna ba.

    Su É—ebo da kaÉ—an-kaÉ—an su ba dai almajiri.

    Inna in ba ki ba ni ba inai maki kukan gada:

    Innaaaaahhhh!

    Inna in ba ki ba ni ba zan yi na saniya,

    Innaaaahhh!

    Inna in ba ki ba ni ba zan yi na tunkiya,

    Innaaaah!

    Inna in ba ki ba ni ba, ni zan kwan a nan.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.