Falalar Ambaton Allah {1}

    Haƙiƙa zikiri ko ambaton Allah yana daga cikin mafiya tsarkakan ayyuka da kyawawansu da girmansu kuma mafiya soyuwa a wurin Allah Azza Wa Jalla. Tirmizi da sauransu sun ruwaito daga Abu Darda’u (RA) ya ce: “Manzon Allah () ya ce: “Ashe ba zan ba ku labarin mafi alherin ayyukanku kuma mafi tsarkinsu (dadinsu) a wurin Mamallakinku kuma mafi daukakawa ga darajojinku kuma mafi alheri gare ku daga ciyarwarku ga zinari da takardun kudadenku ba, kuma mafi alheri gare ku a ce kun hadu da abokan adawarku su doki wuyayenku ku doki wuyayensu ba?” Sai suka ce: “Hakika muna so ka ba mu (wannan labari) ya Manzon Allah!” Sai ya ce: “Zikirin (ambaton) Allah Madaukaki.”

    Masu ambaton Allah, masu tunawa da Allah su ne a kan gaba wurin tafiya don haduwa da Allah da kuma Ranar Lahira lami lafiya. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi () ya ce: “Masu kadaitawa sun wuce gaba. Suka ce su wane ne masu kadaitawa ya Manzon Allah?” Ya ce: “Masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambato (da yawa) mata.” Wadannan su ne -bayin Allah- waɗanda Allah Ya yi musu tattalin masauki mai girma da lada mai girma. Allah yana cewa

     وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا

    Masu zikiri (ambato da tuna) Allah da yawa maza da masu zikiri mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani lada mai girma.”

     

    Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

    الله تعالى أعلم

    ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

    ****************************
    Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
    ****************************

    Telegram

    https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

    WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

    Sheikh Muhammad Auwal Albany

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.