Yaku bayin Allah! ambaton Allah wato zikiri shi ne yake raya zukata, zukata ba su rayuwa sai da shi, Buhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu Musa Al’ash’ari (RA) daga Annabi (ﷺ) ya ce: “Misalin wanda yake ambato ko tuna Ubangijinsa da wanda ba ya ambato ko tuna Ubanginsa kamar misalin mai rai ne da matacce.”
Hakika zukata
ba za su samu tabbatuwa da natsuwa ba, ko su samu jin daɗi su samu sa’ada ba, sai tare da zikirin Allah
da tunawa da Shi. Allah Madaukaki Yana cewa:
الَّذِينَ آمَنُوا وَتَطْمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكْرِ اللَّهِ أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ
. “Waɗanda suka yi imani,
zukatansu suna samun natsuwa ne da ambaton Allah. Ku saurara! Da ambaton Allah zukata
suke samun natsuwa.”.
Ambaton Allah
shi ne ke kawo mafita a bayan kunci, ya kawo sauki a bayan tsanani, ya kawo
farin ciki a bayan wahala da damuwa. Shi yake kwaranye abubuwan da suke kawo
bakin ciki ya saukaka al’amura ya tabbatar da raha da sa’ada a duniya da
Lahira. Babu abin da yake magance bakin ciki ya gusar da tsanani kamar ambaton
Allah da zikirin Allah Madaukaki. Annabinmu (ﷺ)
ya kasance a duk lokacin da wani abin bakin ciki ya same shi yana cewa: “La
ilaha illallahul azim, la ilaha illallahul halim. La ilaha illallahu rabbus
samawati wa rabbul arshil karim.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah Mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai haƙuri.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa
kuma Ubangijin Al’arshi Mai girma.” Sannan Mai Tsira da Amincin Allah yana
cewa: “Addu’ar ma’abucin kifi: “La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz
zalimina.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Tsarkinka ya tabbata,
lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.” Babu wanda zai fada a cikin bakin
ciki da zai yi addu’a da ita face an kwaranye masa bakin cikinsa.”
Ina roƙon
Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai
iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji
na Alƙur’ani
ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai
الله تعالى أعلم
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ
ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ
ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************
Telegram
https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx
WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.