Ticker

Falalar Ambaton Allah {3}

Ambaton Allah yana jawo ni’imar da ta kubuce wa bawa kuma ya kiyaye tare da tsare ni’imar da mutum yake da ita. Kuma babu abin da yake jawo ni’ima ya tsare ta irin zikirin Allah Madaukaki. Allah yana cewa

وَإِذْ تَأَذَّنَ رَبُّكُمْ لَئِن شَكَرْتُمْ لَأَزِيدَنَّكُمْ وَلَئِن كَفَرْتُمْ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٌ

 (“Kuma a lokacin da Ubangijinku Ya sanar, “Lallai ne idan kun gode, hakika (Allah zai) kara muku, kuma lallai ne idan kuka kafirta hakika azabata, tabbas mai tsanani ce.”)

Daga cikin falalar zikiri akwai shafe laifuffuka da kankare miyagun ayyuka da daukaka darajoji da kuma samun daukaka a wurin Allah Madaukaki. Tirmizi ya ruwaito daga Annabi (), ya ce, “Babu wani aiki da dan Adam zai yi da ya fi saurin kubutar da shi daga azabar Allah kamar zikirin Allah.”

Kuma ya tabbata daga gare shi () cewa lallai shi ya ce: “Wanda yace, “Subhanallahi wa bi hamdihi” sau dari an shafe laifuffukansa koda sun kai misalin kumfar teku ne.” Irin wadannan hadisai kan wannan batu suna da yawa.

Sannan daga cikin falalar zikiri akwai cewa, shi shuka ce a cikin Aljanna. Mutum ba ya shuka a cikin Aljanna da abin da ya kai zikiri ko ambaton Allah. Annabi () yana cewa: “Wanda ya ce: “Subhanallahi wa bi hamdihi” za a shuka masa wata dabiniya a cikin Aljanna.” Tirmizi ya ruwaito.

 Kuma Tirmizi (RA) ya sake ruwaitowa daga Annabi (), ya ce: *

Na hadu da Annabi Ibrahim Khalil a daren da aka yi Isra’i da ni. Sai ya ce min: “Ya Muhammad! Ka isar min da gaisuwata zuwa ga al’ummarka, (ya siffanta masa Aljanna, sannan a karshen Hadisin, ya ce,) “Ka ba su labari cewa: “Lallai shukarta ita ce: “Subhanallahi, walhamdulillahi wa la ilaha illallahu wallahu akbar.”

Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

الله تعالى أعلم

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

 ****************************

Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************

Telegram

https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

Sheikh Muhammad Auwal Albany

Post a Comment

0 Comments