Ticker

Falalar Ambaton Allah {4}

Ambaton Allah dai kalmomi ne masu saukin fadi a baki, ba su wahalar da bawa ko su zame masa nauyi, amma kuma suna da lada mai girma da ijara mai yawa. Sannan su kalmomin nan ababen so ne a wurin Allah Madaukaki. Buhari (RA) ya ruwaito a Sahihinsa daga Annabi () cewa lallai shi ya ce: “Kalmomi biyu masu sauki a kan harshe, amma masu nauyi a kan mizani, sannan masu girma a wurin Mai rahama. Su ne: “Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahil azim.”

Sannan zikiri da ambaton Allah na kore shaidanu daga kusa da bawa, na tsare bawa daga wasi-wasin shaidanu da sharrukansu da kaidojinsu da duk miyagun tuggunsu. Allah Madaukaki Ya ce:

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

(“Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaidan, to ka nemi tsari daga Allah. Lallai Shi, Shi ne Mai ji, Masani.”)

Kuma Allah Ya ce:

وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِين / وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحْضُرُونِ

(“Ka ce: “Rabbi inni a’uzu bika min hamazatis shayadini. Wa a’azu bika Rabbi an yahdurun.”)

 (Ma’ana: Ya Ubangijina, ina neman tsari da Kai daga fizge-fizgen shaidanu. Kuma ina neman tsari da Kai, ya Ubangijina! Domin kada su halarto ni.)”

 Kuma Allah Ya sake cewa:

إِنَّ الَّذِينَ اتَّقَوْا إِذَا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِّنَ الشَّيْطَانِ تَذَكَّرُوا فَإِذَا هُم مُّبْصِرُونَ

(“Lallai ne waɗanda suka jin tsoran Allah, idan wani tashin hankali daga Shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah), sai ga su sun zama masu basira.”)

 Kuma Allah Ya sake cewa:

(وَمَنْ يَعْشُ عَنْ ذِكْرِ الرَّحْمَنِ نُقَيِّضْ لَهُ شَيْطَانًا فَهُوَ لَهُ قَرِينٌ 36 ) [الزخرف: 36]

(Kuma duk wanda ya makance ga barin ambaton mai rahama za mu hore masa shaidani sai ya zama abokinsa).

Kuma Allah Ta’ala ya ce,

(وَمَنْ أَعْرَضَ عَنْ ذِكْرِي فَإِنَّ لَهُ مَعِيشَةً ضَنْكًا وَنَحْشُرُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَعْمَى 124 ) [طه: 124]

(Duk wanda ya kau da kai ga barin ambaton Allah mai rahama, to yana da rayuwa mai ƙunci, kuma za mu tashe shi ranar alƙiyama a makaho).

Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

الله تعالى أعلم

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************

Telegram

https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

Sheikh Muhammad Auwal Albany

Post a Comment

0 Comments