Ticker

    Loading......

Falalar Ambaton Allah {7}

Ambaton Allah yana raya gidaje Annabi () ya ce: “Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da gidan da ba a ambaton Allah a cikinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.”

Ayoyi da dama da kuma Sunnar Annabi () suna karfafa mana tare da ingiza mu zuwa ga yin zikiri da ambato da tuna Allah. Kuma suna umartar mu a kan yin zikirin da yawa tare da yi mana bayanin irin ladaddakin da masu yawaita zikiri suke samu a cikin ayoyi masu yawa da hadisai da dama.

Allah Madaukaki Yana cewa:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا

(“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ambaci Allah, ambato mai yawa.)

وَسَبِّحُوهُ بُكْرَةً وَأَصِيلًا

 Kuma ku tsarkake Shi a safiya da maraice.

هُوَ الَّذِي يُصَلِّي عَلَيْكُمْ وَمَلَائِكَتُهُ

Allah Shi ne Wanda Yake yi muku salati (tsarkake ku) da mala’ikunSa (su ma suna yi muku addu’a)

لِيُخْرِجَكُم مِّنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ

domin Allah Ya fitar da ku daga duffai (na kafirci da gafala) zuwa ga haske (na imani da tsarkaka).

وَكَانَ بِالْمُؤْمِنِينَ رَحِيمًا

 Kuma Allah Ya kasance Mai jin kai ga muminai.”

Ibn Abbas (RA) ya ce: “Idan kuka aikata haka – ma’ana kuka yawaita zikiri ko ambaton Allah Madaukaki – Sai Allah Ya yi muku salati (addu’a, Shi) da mala’ikunSa.”

Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa:

 وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا

(“Masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma.”)

Kuma Ya sake cewa:

 وَاذْكُرُوا اللَّهَ كَثِيرًا لَّعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

(“Kuma ku ambaci Allah da yawa, tabbas za ku samu nasara.”) Da sauran ayoyi da hadisai masu yawa da suke kwadaitarwa da karfafa Musulmi su yawaita ambaton Allah kuma suke umartarsu da ambatonSa da yawa.

Ina roƙon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alƙur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin ƙai

الله تعالى أعلم

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​

****************************
Daga: Sheikh Muhammad Auwal Albany Group
****************************

Telegram

https://t.me/joinchat/SoaVkBryƙONVNGyU8dDpLƘzx

WANNAN YA ZO MUKU NE DAGA SHEIK ALBANY DA’AWA GROUP. Ga masu son shiga wannan group ko turo da tambaya, to suna iya tuntuɓar wannan lambar ta Whatsapp: 08179713163.

Sheikh Muhammad Auwal Albany

Post a Comment

0 Comments