Gabatarwa – Daga Littafin “Bara Da Wasu Waƙoƙin Bara A Ƙasar Hausa”

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin Samun Cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Gabatarwa

    Bara wata ɗabi’a ce wadda take gudana a cikin al’umma wadda ta yi mana katutu a tsakaninmu har ma take neman ta janyo mana reni daga wasu al’ummomin waɗanda ba Hausawa ba. Bara ya sa ana yi wa Hausawa kallon hadarin kaji suna ɗaukar Hausawa koma-baya! Wannan damuwar ce ta sa aka yi tunanin rubuta wannan littafin domin fayyace wannan lamarin ga ‘yan’uwana ɗaliban ilmi da shuwagabanninmu da kuma gwamnatoci. An yi haka ne domin ƙara fahimtar lamarin a fuskance shi ta hanyar da ya kamata. Karanta wannan littafin kan warware wa wasu al’ummun kansu, su daina ɗaukar cewa kowane Bahaushe mabaraci ne kafin ya zama abin da ya zama.

    An bi hanyoyi da dama wajen tattara bayanai a lokacin aikin wannan littafin kamar su shiga a ɗakunan karatu manya da ƙanana a manyan jami’o’inmu na arewacin Nijeriya da kuma kwalejojin ilmi da sauran wasu muhimman wurare domin samun ayyukan waɗansu magabata a kan abin da ya shafi bara.

    Bayan wannan an sami ganawa da jama’a daban daban tun daga almajiran har naƙasassu maza da mata don samun ingantattun bayanai. An ziyarci makarantun allo da wasu wuraren da almajirai ko mabaratan sukan yi dandali kamar tashoshin mota da kasuwanni da gidajen karuwai da wajen buki har ma da tituna da lunguna don haɗuwa da irin waɗannan mutanen a gana da su.

    Ba su kaɗai aka sami ganawa da su ba, an gana da lafiyayun mutane kamar malamaina da malamansu da kuma abokan arziki waɗanda suka san sha’anin bara na gida da waje.

    Littafin ya ƙunshi babubbuka guda takwas ne a babi na farko an yi shimfiɗa ne inda aka gabatar da bara ga makarantan littafin don su san babban batun da ya haifar da rubutunsa. Babi na biyu ne ya bayyana yadda baran yake a ƙasar Hausa ba kamar yadda wasu suke ɗaukarsa ba. A babi na uku ne littafin ya mayar da hankalinsa ga masu yin baran a ƙasar Hausan domin a tantance su. Shi kuwa babi na huɗu waƙoƙin bara ne wato waɗanda ake amfani da su wajen baran aka kawo. Babi na biyar ya taɓo sigogi ne da falsafar waƙoƙin bara domin a bambance aya da tsakuwa. A babi na shida kuwa aka kawo jigogin waƙoƙin baran tare da zaƙulo misalai mabambanta daga waƙoƙin na bara. Ba a taɓi salo ba sai a babi na bakwai a wannan littafin inda aka bayana shi da kuma zubi da tsarin waƙoƙin na bara. Sai babi na takwas kuma na ƙarshe inda aka kawo rabe-raben waƙoƙin baran, kasancewar a babukan baya an zaƙulo waɗansu wurare ne daga cikin waƙoƙin, sai aka kawo kammalallunsu a wannan babin don daɓen ya ji makuba. Allah ya sa a amfana da shi. Amin ya Hayyu ya Ƙayyumu. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.