Gamshe

    Gamshe ciyawa ce mai kyau musamman a wajen masu kiyon dabbobi

    Gamshe tana cikin ciyawa da doki ya fi daso fiye dakowace ciyawa awajen Æ™otonsa

    Gamshe ciyawa ce dabaka samunta a kan sahara sai dai a fadama wajen da ke da Dausayi musamman bakin Tafki ko korama ko kuma bakin kogi/rafi

    Gamshe ciyawa ce gwanin sha'awa za ka same ta tsanwa shar/koriya,

    Gamshe takan yi Æ™onshi ya fitar da kai fari idan ya Æ™osa kaman kansu kusan É—aya da kan rake, sai dai kansa bai kai na rake girma da fadi ba, amman duk kansu fari fat maikama daya.

    Gamshe ciyawa ce da Doki yake ci sosai amman dabbobi kaman su shanu da tumaki da awaki da jakai da rakomi Duk sunacin Gamshe

    Yakan fito ne a lokacin damina idan rani yakama yakan chanza kala daga tsanwa/kore zuwa É—orowa  É—orowa dagan nan dai idan rani yayinisa yabushe Æ™omomus

    Gamshe masu dabbobi sukan yanki ciyawa Gamshe da damina suke baiwa Dabbobinsu idan rani yayikuwa sukan rinka tonon sayyunsa akaima dabbobin da muka ambata asama

    Gamshe kunnuwansa tsanwaye ne/koraye karansa kuma yanada ga'ba ga'ba, kaman karan gero ko Dawa, ko wata ciyawa da muke kira da suna ILLiri, kunnuwansa da ga'bo  'binsa tsanwaye ne/koraye sai dai Sayyunsa farare ne fat

    Gamshe sayyunsa sunada zaƙi zaƙi, hakama karansa, sai dai kunnuwansa sukan yanka mai aikin yankansa kaɗan kaɗan saboda sunada dan kaifi

    Gamshe akansame shi acikin fadamar kanwa ta gefen yankin Gobirawa, Sabon birni L/G Sokoto State, takan yuyu asameshi acikin fadammu dayawa a kowane yankin,

    Gamshe muke kiransa a namu yankin takan yuyu wasu sukan kira shi da wani sunan daban ba Gamshe ba.

    Gamshe

    Daga Taskar

    Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
    Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.