Ticker

6/recent/ticker-posts

Gidan Sarautar Bakura

 Gidan Sarautar Bakura

Gidan Sarautar Bakura

"Bakura mun biya, mu kawa Tudu murna Bakura an naɗa sabon Sarki" cewar Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan Anace Yar Tsakkuwa, Gandi Sakkwato a faifansa na Ɗan Dambe Miko Dogo. Makaɗa Ɗan Anace na nufin da ya taso daga garinsu na Yar Tsakkuwa dake cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Raɓah ta Jihar Sakkwato babban garin da ya fara yada zango shi ne Bakura wadda ke cikin Jihar Zamfara ta yanzu domin ya taya Dagacin Birnin Tudu, watau Tudun Birnin Tudu, Marigayi Alhaji Tukur murnar zamowar Yayansa/Wansa, Marigayi Alhaji Muhammadu Mai lafiya Sarkin Ɓurmin Bakura /Uban Ƙasar Bakura/Hakimin Gundumar Bakura a lokacin. Ya yi sarauta a Bakura daga shekarar 1970 zuwa lokacin da aka cire shi a shekarar 1980/81. Wannan shi ne gidan Sarautar Bakura. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815

Post a Comment

0 Comments