Godiya - Daga Littafin “Bara Da Wasu Waƙoƙin Bara A Ƙasar Hausa”

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin Samun Cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Godiya

    Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai wanda ya nufe ni da rubuta wannan littafi a kan sha’anin bara a ƙasar Hausa. Ina kuma miƙa cikakkiyar godiyata ga iyayena waɗanda suka taimaka mani tun ban san bihin[1] ba har na tasa, suka sa ni a makarantu daban-daban na karatun addini da na boko har Allah ya kawo ni yanzu inda nake, Allah ya yi masu sakayya da gidan aljanna, amin. Ina kuma godiya ga malamina jarumi wato Farfesa Atiku Ahmad Dumfawa wanda ya duba wannan littafi tare da yin gyare-gyare a cikinsa don ƙara inganta shi ya zama abin amfani ga al’umma baki-ɗaya, Allah ya biya shi. Ina godiya ga Dr. Isah Bala Homawa wanda ya saba bani ƙwarin guiwar tafiyar da harkokina na cigaba ya kuma saba taya ni bincike na dukkan wani abu da ya ɗaure man kai, Allah ya biya shi. Ba zan manta da abokaina ba waɗanda suke ba ni shawarwari a kan wannan aiki tun farko har ƙarshe, kamar su malam Bashir Aliyu Tsafe da malam da Almustafa S/Fulani Bunguɗu da Idris Abubakar Bunguɗu da Abdullahi Abubakar Bunguɗu da malam Ibrahim Ahmadu Ɗan’amarya da dai sauran waɗanda ban samu kawo sunayensu ba. Na gode Allah ya haɗa mu a aljanna Firdausi baki-ɗaya. Allahumma amin.



    [1]  Idan mutum bai kama karatu ba ko yana ɗanyaro bai gane ta kan duniya ba ana cewa bai san bihin ba. Wato bai san daidai ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.