Hukuncin Azumin Kaffara Ga Mace Mai Al'ada

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Macece take tukin mota saita kade mutum yaya za ta yi azumin kaffara saboda mace tana al'ada duk wata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Kaffarar kisan kuskure ita ce: 'yanta baiwa da biyan diyyah, ko azumin wata biyu ajere, wanda bai samu abun da zai 'yanta baiwa da shiba ko yayi azumi sittin ajere ba, babu laifi agareshi, ba'a ciyarwa akaffarar kisan kuskure abisa mafi rinjayen maganganun malamai.

    Allah maɗaukakin sarki ya ce

    وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَنْ يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَأً ۚ وَمَنْ قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَىٰ أَهْلِهِ...

    Bai halatta ga mumini yakashe ɗan'uwansa mumini ba saifa inda kuskure, duk wanda yakashe mumini tahanyar kuskure kaffararsa shi ne ya 'yanta baiwa mumina dakuma diyyah dazai mika ga ahlin wanda yakashe.

     ... ۖ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِنَ اللَّهِ ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا

    Duk wanda bai samuba sai yayi azumin wata biyu ajere dan tuba ga Allah, Allah yakasance masani mai hikima.

    Saboda haka idan azumin wata biyu yahau kan mace mai al'ada, Saita fara azumin tana cikin azumin sai jinin Al'ada yazo mata, to azuminta nawata biyun bai yankeba, zata sha azumin sannan saita rama kwanakin datayi hailar, saita dora lissafi tacika wata biyun, domin haila wani al'amarine da Allah yadorawa mata ita, bata da iko akai, wannan ijma'ine atsakanin malamai.

    Ibnu ƙudama rahimahullah acikin Almugni ( 8/21) ya ce

    " malamai sunyi ijma'i akan mace mai azumin wata biyu ajere, idan haila tazo mata kafin ta kammala, zata rama kwanan hailar idan tai tsarki, domin haila baza'a iya kauce mata acikin wata biyu ba, saidai idan zata jinkirta harzuwa tadaina hailar, wannan kuma zaikai ga azumin yashiga garari bazata samu damar yin saba"

    Misali ace zatai azumin kaffarar awatan muharram da safar kuma kowanne acikinsu hailarta kwana bakwai ce, to zata sha azumin waɗannan kwana bakwai ɗin nakowanne wata, saita ramasu dazarar watan safar yakare, babu jinkiri saitayi azumi goma sha huɗu ajere, nafarkon watan rabi'ul Auwwal.

    Wallahu A'alamu.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.