Hukuncin Kallon Fina-Finan Batsa (Blue Film)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Salam Malam Menene hukuncin magidancin da ya ke kallon film ɗin dake nuna tsiraici da matarsa a musulunci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalamu warahmatullah.

    Inna lillahi wa inna ilaihi raji’una, lallai al’umar musulmi mun samu kanmu a halin koma baya da tabarbarewar dabi’u. Amma Annabi yayi gaskiya, inda ya ce: lallai za ku bibiye halaye irin na mutanen da suka gabaceku.

    Baya hallata ga musulumi kallon fina-finan da ake nuna tsiraici, ko hutunan da ke baiyyana tsiraici, ko kallon tsiraicin a zahiri, mutum shi kaɗai ne ko tare da matarsa ta Sunnah.

    Al-kur’ani mai Girma yana cewa a cikin Suratun-Nūr:

    قُلْ لِلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَزْكَىٰ لَهُمْ ۗ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا يَصْنَعُونَ

     Ka fadama muminai maza su rintse idanuwansu kuma su tsare farjinsu. Wannan shi ne yafi tsarki agaresu, kuma Allah mai bada labarin abin da suke aikatawa ne. (Suratun-Nūr Ãya ta 30)

    وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ ...

    Kuma ka fadawa muminai mata su ruitse idanuwansu kuma su tsare farjinsu… (Suratun-Nūr Ãya ta 31)

    Wannan umurnin Allah ne ga duk wani mumini, don haka musulmin kwarai ya rintse idon sa daga kallon tsiraici wajibi ne. Babu saɓani acikin haka agurin magabata.

    Kallon tsiraici yana kekasar da zuciyar mutum, kuma yasa shi yazama raukananne ga barin Allah da ambatonsa. Kamar yadda yake gadar da ciwukan zuciya da na ruhin Ɗan-Adam, sannan kuma ya nisantar dashi daga halal kuma ya kusantar da shi zuwa ga haram da miyagun ayyuka.

    Ya ku ‘yan-uwa magidanta, Annabi ya yi umurni da suturta tsiraici kuma ya yi hani da bayyana tsiraici ko kallon tsiraicin. Saboda bala’in da dake cikin hakan.

    Ba ya hallata ga wani yaga tsiraicin wani saidai ma’aurata, ko akan matsananciyar lalura. Amma abin da magidanta ke fakewa da shi na kallon fana-finan batsa da tsiraici- wai cewa suna koyon salon jima’i da hanyoyinsa ko kuma su ce, yana mutsar da sha’awarsu- to wannan ba zai taɓa zama hujja a gurin Allah ba, domin saɓawa umurninsa ne.

    Kallon fana-finan batsa da tsiraici tafarkin sheɗan ne, yana amfani da shi don halakar da magidanta. Al’hali kuma Allah da Manzonsa sun yi umurni da rintse ido daga kallon tsiraici.

    Duk wasu magidanta da ke kallon fana-finan batsa da tsiraici, to su tuba zuwa ga Allah, kuma su bari, tun kafin mutuwa ta riske su.

    Ya Allah, Ka tsare mana Imaninmu da Mutuncinmu. Amin.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hZ6HoDt65aKhhKOiDpZ

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.