𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Mene ne hukuncin macen da take yawan fita agidan mijinta koda saninsa ko bada saninsa ba? Mene ne kuma dalilai daze sa mace tafita agidan bissa karantawar sunnar Annabi (S.A.W) ? Wassalam
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus
salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Haramun ne ga
Mace ta fita gidan ta ba tare da izinin Mijin ta ba. Yin haka babban kuskure ne
ga shari'ar Allah. Duk matar dake fita ba tare da izinin mijinta ba, fushin
Allah yana samunta har sai ta dawo ta nemi yafewarsa. Allah ya haramta fita
waje ga Mata waɗanda
aka yiwa sakin kome (saki 1 ko 2) ballantana waɗanda
suke matan aure ne ba'a sake su ba. Allah maɗaukakin
sarki Yana cewa a Suratul Ɗalaaƙ aya ta 1:
ﻳَﺎ ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲُّ
ﺇِﺫَﺍ ﻃَﻠَّﻘْﺘُﻢُ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀَ ﻓَﻄَﻠِّﻘُﻮﻫُﻦَّ ﻟِﻌِﺪَّﺗِﻬِﻦَّ ﻭَﺃَﺣْﺼُﻮﺍ ﺍﻟْﻌِﺪَّﺓَ ۖ ﻭَﺍﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ
ﺭَﺑَّﻜُﻢْ ۖ ﻟَﺎ ﺗُﺨْﺮِﺟُﻮﻫُﻦَّ
ﻣِﻦْ ﺑُﻴُﻮﺗِﻬِﻦَّ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺨْﺮُﺟْﻦَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻥْ ﻳَﺄْﺗِﻴﻦَ ﺑِﻔَﺎﺣِﺸَﺔٍ
ﻣُﺒَﻴِّﻨَﺔٍ ﻭَﺗِﻠْﻚَ ﺣُﺪُﻭﺩُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ۚ ﻭَﻣَﻦْ ﻳَﺘَﻌَﺪَّ
ﺣُﺪُﻭﺩَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﻘَﺪْ ﻇَﻠَﻢَ ﻧَﻔْﺴَﻪُ ۚ ﻟَﺎ ﺗَﺪْﺭِﻱ
ﻟَﻌَﻞَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳُﺤْﺪِﺙُ ﺑَﻌْﺪَ ﺫَٰﻟِﻚَ ﺃَﻣْﺮًﺍ.
FASSARA:
Ya kai Annabi!
Idan kun saki mãtã saiku sake su ga iddarsu, kuma Ku ƙididdige iddar. Kuma kubi
Allah Ubangijinku da taƙawa. Kada Ku fitar dasu daga gidãjensu, kuma kada su fita fãce
idan sunã zuwa da wata alfãsha bayyananna. Kuma wadancan iyãkõkin Allah ne.
Kuma Wanda ya Ketare iyãkõkin Allah, to, lalle ya zãlunci kansa. Baka sani ba
dammãnin Allah zai fitar da wani al'amari a bayan haka.
Manzon Allah ﷺ Yana cewa: Na horeku da
yin adalci wa matanku, domin cewa su Fursunoni ne agareku. Saboda haka mace
kamar baiwa ce ko yar fursuna ga mijinta, kuma bazata fita gidansa ba saida
izinin sa. Koda Mahaifinta ko Mamanta ko wani na daban sun umarce ta da aikata
hakan a bisa ra'ayin jumhurin malamai.
(Al-Fataawa
Al-Kubra, 3/148).
Ibn Muflih
al-Hanbali ya ce: Haramun ne ga mace ta fita wajen gidan mijinta ba tare da
izininsa ba, sai fa a yanayi na larura ko wajibcin shara'ah. (Al-Adaab
Al-Shar’iyyah, 3/375)
Imamul Ƙurtubiy
ya ce "idan har buƙata ta sanya za a fita ɗin,
to lallai ne fitar ta kasance cikin kulawa tare da cikakken suturce jiki"
DAGA CIKIN
MANYAN DALILAN DA ZASU IYA JAWO FITAR MACE DAGA GIDAN MIJINTA AKWAI:
1. NEMAN
ILIMIN ADDINI: idan har mijinta bashi da ilimin da zai koya mata ibadah, kuma
ba zai iya dauko wata macen da zata koyar da ita a gida ba, Kuma shi kansa
bashi da malamin da zai koyar dashi sannan ya dawo ya koyar da iyalinsa da
kansa.
Kuma wajibi ne
koyon ilimi ya zamanto awajen mace 'yar'uwarta zata koya. Idan kuma duk garin
babu matar dake da ilimin da zata koya awajenta, shike nan sai mataye da yawa
su taru awaje ɗaya
sannan a nemo namiji mai ilimi, mai tsoron Allah wanda zai karantar dasu ba
tare da sun gan shi ko shi ya gansu ba. (wato a sanya labule atsakaninshi
dasu).
2. NEMAN
LAFIYA: Idan ba ta da lafiya ya halatta ta fita zuwa asibiti domin ganin
likita.
3. ZUMUNCI: Ya
halatta ta rika zuwa tana gaida mahaifanta ko makusantanta (kamar Ƙannai
ko yayun iyayenta) idan buƙatar hakan ta taso. Wannan ya haɗa
har da ta'aziyyah da duba marar lafiya.
4. BAYAR DA
SHAIDA: Idan wani abu ya faru wanda ake buƙatar matar taje ta bayar da shaida a
gaban alkali ko wata hukuma.
5. SANA'A: Ya
halatta ta fita taje tayi sana'a idan har mijinta ba zai iya ɗaukar nauyinta ba, Kuma ba
ta da wani wanda zai taimaka mata. Amma wajibi ne sana'ar ta zamto halastacciya
kuma babu cudanya ko keɓancewa
da mazaje acikinta.
6. FITA DOMIN
HALARTAR SALLAH: Yana zama halal idan har zasu fita bisa cikakken lullubi tare
da rashin keɓancewa ko
cuɗanya da maza. Ya
halatta su halarci sallar Eidi ko Jumu'ah, har sallolin farilla a masallaci
amma akwai Ƙarin
wasu Ƙa'idodi
da malamai suka ajiye.
Amma fita don
yin cefane ko kaiwa yara makaranta, wannan hakkin namiji ne. Bai halasta mace
ta fita musamman domin yinsu ba, sai dai bisa larurar rashin miji, ko wani
Muharrami wanda zai isar mata.
WALLAHU A'ALAM
Fatawowi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.