Hukuncin Mijin Da Yake Sa Wa Matarsa Hannu A Farjinta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Malam tambayata anan shine, meye hukunci mijin da se yasawa matarsa hannu a farjinta duk da an ce yana kawo warin gaba, kuma Dan Allah ataimakawa afada mana magani buɗewar ‘ya mace, da maganin da za ta dinga sha malam wlh ƙawata tana cikin wani hali gurin mijinta, shine tace na taimakamata tunda ina cikin wannan gida me albarka wasalam mun gode da jajirce mana da koyar da ake mana bisa turba musulunci

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumussalam warahmatullah

    Sa hannu agabanta balaifi ba ne sai dai ya tabbatar da tsaftan hannunshi sosai saboda gudun kwasan kwayoyin cuta.

    MAGANIN BUƊEWAR 'YA MACE:

    Ki sami sassaken bagaruwa/gabaruwa da ‘ya’yanta kina tafasawa kina zama a ciki ki yi kaman 30minutes safe da kuma yamma kuma da dumi zakina shiga kaman 2weeks, ki bar zama babu pant, ki daina tsarki da ruwa mai sanyi kuma ki sami ganyen magarya ki tafasa ki shiga kullum sau ɗaya na kwana uku, ki guji cushe-cushe na maguna da sunan matsi, ki rika tsaftace gurin kina shafa farin miski ko da a pant ne, ba sai kin tura ciki ba.

    In kuma kin taɓa samun kari ne a gurin yayin wata haihuwa kuma ba a dinke ba, to babu magani da zai mai da ki daidai sai kin koma an ɗinke ko da kuwa ya yi shekaru.

    WALLAHU A'ALAM

    Ameenah G. Mukhtar

    Momin nasreen

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.