Hukuncin Yi Wa Karuwai Gyaran Jiki

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, malam don Allah ina da tambaya, mace ce ke sana'an lalle da kitso da gyaran jiki shin ya halatta ta yi ma karuwai? na gode Allah ya kara basira.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah wa Barakátuhu, Allah Maɗaukakin Sarki a cikin Alƙur'ani mai girma ya yi umurni da mu yi taimakekeniya a wurin aikin kirki da tsoron Allah, kuma ya hana mu yin taimakekeniya a wurin saɓo da ƙetare iyaka (zalunci) a aya ta 2 da ke Suratul Má'ida.

    Gyara wa maɓarnata hanyar yin ɓarna da ƙara ƙawata abin da ake ɓarnar da shi, yin hakan ma ɓarna ce, su karuwai suna yin amfani da jikinsu ne wurin aikata alfasha tare da kwastamominsu maɓarnata, to bisa dogaro da waccan ayar ta Suratul Má'ida da Allah ya hana yin taimakekeniya wurin saɓo, sai ya zama bai halasta mai sana'ar gyaran jiki ta riƙa gyarawa karuwai jikinsu ba, musamman idan ya kasance abin da take gyarawar yana taimaka wa muguwar sana'arsu ta karuwanci, saboda yi masu gyaran jiki taimaka masu ne wajen su yi kasuwa.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.