Ticker

    Loading......

Hukuncin Yin Sallah Da Lalle A Jiki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah ya ƙara wa malam lafiya da imani, malam tambayata ita ce shin mutum zai iya yin sallah da lalle a kansa, kuma zai iya yin sallah bayan ya sanya tafarnuwa a al'aurarsa? Na gode sosai Allah ya ƙara taimakonmu ya azurta mu da kyakkyawan ƙarshe.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, ƴar uwa lalle ba najasa ba ne, idan mace ta yi sallah da shi a kanta ko a jikinta sallarta ta yi, amma dole ta kasance ta yi alwala ne kafin ta sanya lalle ɗin, amma kuma duk da haka ta yi abin ƙyama. In da ace lalle najasa ce to da zai zama sallarta ba ta inganta ba sai ta sake yi

Bai kamata mace ta sa lalle a lokacin sallah ba, abin da ya fi kyau ta bari sai dare ya yi, bayan sallar Isha'i sai ta sa lalle ɗin a jikinta, kafin Asubahi ya bushe ta cire shi. Haka nan sallarta ta yi ko da ta sa tafarnuwa a al'aurarta saboda maganin wata cuta, saboda ita ma ba najasa ba ce, yin sallah da abu mai najasa a jiki shi ne ke ɓata sallah.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments