Idan Soja Ya Kashe Ɗan Kasa A Wajan Tarzoma, Zai Yi Kaffara !

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Warahmatullah. Don Allah mene ne Hukunci a kan harbe mutum da Jami'an tsaro suke yi Fagen aikinsu. Misali: Idan Soja ya kashe mutane domin ya kare Najeriya, ko Ɗan sanda a wajen kwantar da Tarzoma ya kashe mutane bisa Umarnin Gwamnati domin a samu Zaman Lafiya a cikin Al'umma? Ko kuma Kwastam idan ya Harbe masu Fataucin abubuwan da Najeriya ta hana shigo da su, ya yi aiki bisa Dokar Ƙasa kenan. to mene ne Hukuncin wannan ki saka da ya yi a Musulunci? Na gode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam. Mutukar Ɗan'taadda ne, ko Kuma ya Saɓawa dokokin kasa da suka kunshi maslahar dukkan Al'uma, in an tabatar da su, to ba shi da laifi in ya kashe shi, saboda dimbin hadisan da suka halatta kashe 'yan ta'adda da masu kokarin raba kan Al'uma.

    Ya wajaba jami'an tsaro su guji harbin Mai uwa da wabi, ko na kabilanci ko kuma Harbin mutum saboda ya ki saituwa ko kuma bada rashawa, Allah Yana cewa a suratun Nisa'i Aya ta (93):

    وَمَنْ يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا

    Kuma wanda ya kashe wani mũmini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Yã yi fushi a kansa, kuma Ya la´ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azãba mai girma.

    "Kashe mumini ɗaya ya fi girma a wajan Allah fiye da gushewar duniya", Kamar yadda Baihaky ya rawaito a hadisi Mai lamba ta: (3448).

    Annabi Yana cewa "Duk Wanda ya kashe kafirin Amana ba zai ji kamshin Aljanna ba" Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi Mai lamba ta (2995).

    Allah ne Mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.