Iyaye Don Allah Ku Taimaki 'Ya'yanku Wajen Neman Halal - Su Daina 'Kwacen Waya

    lyaye da yawa yanzu sun daina neman sanin inda y'ay'ansu maza da mata suke samun kuÉ—insu na rayuwar yau da kullum. Sa6anin iyayenmu na da da suke masu gudun haram ta kowanne fanni.

    A da daga miji har mata kowa na sa ido suna jan hankali da tunatarwa juna jin tsoron Allaah da gujewa cin haram ko kawo samu na haram gida har iyali da yara su ci a ciki. Amma ban da yanzu. Duk an zama ja haÉ—e a cin haramun.

    Maza da yawa sun daina damuwa da hanyar samun abincinsu don ko shakka babu mafi akasarinmu yanzu mun koma "Yaki haram yaki halal". Kusan ma neman haram É—in ya fi yawa. Halal kuwa in ya ga dama ya zo in ba haka ba ko oho.

    Mata a yanzu fa da yawa ba su ma san akwai bambanci tsakanin miji ya nema musu abinci, sutura, muhalli ko abubuwan sarrafa rayuwa ta hanyar halal ba. Kun ga tunda ba su san shi ba to ta yaya za su nemi a kawo musu halaliya?

    To tunda mata da yawa-yawansu sun daina tunatar da mazajensu na aure nemo halal, kusanma da yawa sun ajiye nauyinsu na kula da gida da yaransu sun koma nemawa kansu kuÉ—i ta kowane hali, yanzu dai ma iya cewa kiyaye haram kusan dai babu shi illa É—is.

    Baban burin da yawan magidanta a yau shi ne mu tabbatar matanmu ba sa yi mana ƙorafin babu. Shi ya sa duk abinda za mu yi za mu yi don mu kawo na sawa a bakin salati. Halal ne ko haram duk bai dame mu ba muddun dai matanmu za su sakan mana mara.

    Su kuwa matan saboda sa ido akan abun duniya kullum ba su da natsuwa ko wadatar zuci. Ga kuma renuwa ta yi musu katutu. Ko da yaushe babban burinsu shi ne nasu ya fi na wacce. Tunda kuma abin da mazajensu ke kawowa ba ya isan su to kowacce ta yanke shawarar ta fita da kansu nema don cike gi6i.

    A yayin da hakan ke kasancewa kar fa mu manta cewa wata gagarumar 6araka ce ke samuwa dalilin barin gida ta tafi neman aiki a kwararo da matar nan wacce ita ce uwar yaransa ke yi don neman maye gurbi.. Kun ga ke nan dukkan abubuwan da mata da uwa kan yi don a samu ingantaccen gida babu mai yinsu ke nan.

    Sai dai kash! wAllaahi illar ba a nan kawai take ba. Babbar cutarwar da hakan kan haifar yana tattare ne da abinda yake faruwa ga abubuwan da matar mutum uwar y'ay'ansa ta tsallake ta bari. Kun ga matsalar kwacen wayar nan da yanzu haka ya damu kowa to kar ku raba É—aya biyu tushensa ke nan.

    In zan maida mu baya kaÉ—an kan batun neman halal da ciyar da kai da ahali shi, uwayen yanzu da suka ajiye tuhumar mazajensu samo halal to haka ma yanzu da wuya ka ji uwa na tambayar É—anta ko y'arta ina suke samun kuÉ—in da suke kashe mata, na halal ne ko na haram? Duk an daina wAllaahi.

    Abinda da yawa ba a la'akari da shi shine gudummawar da uba na gari musamman ma uwa ta gari kan bayar ga al'uma wajen reno da tarbiyantar da sahihan maza da mata masu hankali, ƙima, daraja da kamala ban da uwa uba tsoron Allaah, Ubangiji Allaah SWT ne Kaɗai zai iya saka musu.

    Kun ga uwa ta gari da Gwamnati za ta san darajarta da fa'idarta wajen yayewa al'uma matsalolin da kan addabi bani Adama wAllahi da wani kaso na musamman hukuma za ta ware mata don biyanta albashi duk wata. Wai don karma ta dinga yin komai illa kawai reno da tarbiyar yara manyan gobe.

    Amma sai ta kasance Gwamnatin ma ba ta san haka ba balle a ce mazanjensu, iyayen y'ay'ansu su sani. Har ta kai suna wulaƙanta matansu suna sa su shiga cikin ƙunci da halin ƙaƙa-na-ka-yi. Yanzu ga shi nan da yawa matan na ajiye nauyin da Allaah SWT Ya ɗora musu suna shiga gari fafutuka.

    Illar wannan al'amarin kuwa yanzu akan wa yake ƙarewa? 'Ya'yanmu. Ƙanenmu. Sai kuma akan dukkan al'uma! Ga misali nan a musibar ƙwacen wayar nan. Wata uwa ce da aka kashe mata ɗa mai ƙwacen waya na ji ta a rediyo tana fargar jaji tana cewa sun rabu ƙalau ranar mutuwarsa. Amma ko ta tambayi me yake yi? Ba na jin ta sani. Allaah dai Ya gafarce mu.

    Yara ne matasa masu ƙarfi a jika sun kai munzalin su yi aure su riƙe mata da yara wato jikokin wasu amma rashin gina musu tsoron Allaah da gudun hisabi da iyaye yanzu ba sa yi gami da rashin aikin yi duk da wasunsu na da ilimin boko da na addini daidai gwargwado ya sa suke zama y'an ta'addan dole. Ba sa ko tsoron komai ya tafasa ya ƙone.

    Yanzu ga shi an dawo ana neman mafita. Yaran nan saboda rashin tarbiya, imani, tsoron Allaah, rashin ilimi na boko da na islama da kuma rashin amfani da shi, rayuka sai salwanta suke yi. Dukiya sai asararta ake yi. Duk akan me? Wani abinda bai taka kara ya karya ba... Waya!

    ©2023 Tijjani M. M./DWi/SWS Radio RagaÉ—aÉ—au/SWS.Comms

    Daga Taskar

    Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
    Imel: mmtijjani@gmail.com
    Lambar Waya: +234 806 706 2960

    A Kiyayi Haƙƙin Mallaka

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.