Ticker

Kishi Rahama Ne Ko Azaba // 38

KISHI A DA DA YANZU: Akwai bambanci sosai tsakanin yadda maza ke iya magance kishi a tsakanin matansu a da, da yadda muke yi a yau, nesa kuwa ba ma kusa ba, domin duk kishin da mata ke yi a da suna tsoron uwayensu kar maganar ta kai musu, kamar yadda suke tsoron mazajensu su same su suna tsakiyar jidali, shi ya sa ko suna abinsu in lokacin dawowar maigidan ya matso sukan shiga taitaitayinsu.

Da kishin da komai, da daɗi ba daɗi, za su rayu a gida daya ga daki - ga daki, sukan yi habaice-habaicensu, su jefa wa juna magana wata har ta yi kuka saboda mummunan abin da aka fada kan uwayenta, amma da wahala matuƙa ka ji ta dauki makami wai za ta kashe kishiyarta, ko shi maigidan kansa a dalilin kishi, to bare a ce ta fara tunanin yadda za ta kashe kanta. A 'yan shekarunnan na tsakiya ne Hausa/Fulani suka fara hada mata sama da daya a gida daya wasu ka samu falo daya ne da su ƙwallin-ƙwal, ba a cewa babu kishi amma ana rayuwa a hakan ba tare da an ji maganar ƙona daki ko zubar da jini ba.

Sai lokacin da wadata ta fara samuwa, ilimin raba mata ya fara yawaita sannan aka fara raba matan, kowace mace za ta zauna a gidanta ita kadai ba tare da kishiya ba, sannan ne daga baya aka fara gane cewa ko a shari'an ma akwai fahimtar da ta fi ƙarfafa raba matan don samun damar zama lafiya da kawar da kishi a tsakaninsu, da ma iya hada kan 'ya'yansu.

Nakan ce: Idan maigida yana ƙarfin da zai iya auren mata hudu, kuma ya yi wa kowa daga cikinsu gidanta na daban, hakan shi ya fi, don ba su hadu ba ma bare wata ta saka dayar cikin tashin hankali. Koda shekarun da dan dama amma zan ita tuno amaryar ta shigo da zafi ta yi ƙoƙarin fitar da uwargidar, ashe kallon kitse take wa rogo, uwargidar mahaukaciyar gaske ce, ƙarshe sai da ta nemi a shiga tsakaninsu ta kasa ja da ita. Mazan yanzu mun san yadda za mu tara mata da yawa, amma ba mu koyi yadda za mu tafiyar da su ba, ba yadda za ka tara mata ka zuba musu ido ka ce su je su zauna lafiya.

In dai ka auro yarinya ƙarama to dauke ta ka kai ta can nesa, ka riƙa kiyaye sha'anunnukan da za su hada su tare, in wata za ta je wannan to dayar sai wani sha'ani idan ya taso. In kana da manyan yara da uwargidan ka nuna musu cewa kai ka haife su duk wace ka aura kuwa daidai take da uwarsu, ba za ka taba ba da barakar da za a raina ta ba. Da haka za ka kiyaye mata mutuncinta, ka kare ta daga masifar kishin da wani lokacin yake hade da rainin arziƙi. Galibi in ka ga mutum ya tsufa amma ya auro ƙaramar yarinyar da ba ta wuce tsarar diyarsa ba, da wahala ka ga ba mai hannu da shuni ne ba.

Ba cewa nake hakan kuskure ne ba amma ya san yadda zai kare mata mutuncinta a gabar uwargidarsa da 'ya'yanta, in ba haka ba zai ci amanar uwayenta da suka aura masa. Na ga amaryar da wani Alhaji ya auro, duk in aka ce sun hadu a gidan sha'ani sai uwargidar ta hadu da ƙawayenta suna nuna amaryar suna dariya, sai zagi, habarci da muna nan maganganu kuma ba ta isa ta yi magana ba su yi mata tijarar da ko kare ba zai ci ba, duk cikinsu ba wace ba ta haife taba. Haka za ta zo ta gaya wa maigidan irin cin-kashin da suke mata a maimakon ya yi wani abu sai dai ya ba ta haƙuri kawai ya ce ta daina kula su zafin kishi ne kawai, ba tare da ya yi mata maganin halin da take ciki ba.

Sai da yarinyannan ta fara lalacewa, uwayenta suka fara surutai sannan ya dauki matakin da ya kamata. Maza ke nan a yau, maganar gaskiya uwayenmu na dauri sun fi na yanzu iya maganin kishi. Ina yaro na taba gani maigidan dake yi wa matansa dukan tsiyavin ya tarar suna fada, kuma ba abin da zai faru. Sai dai kowa ta ƙarisa kukanta ta koma dakinta, in ma za su ci-gaba to sai dai in ba ya gida, yanzu na san hakan ba zai yuwu ba saboda ilimi ya yawaita, kuma an dauki wayewar da ba tamu ta asali ba, uwayen matan na iya maka surukin nasu a kotu, ko ba haka ba ma ƙanninta ma za su iya nakada masa dukar tsiya.

Don wani ya gaya min cewa da aka fitini yayarsu ƙanninsu suka sami mijin suka yi masa jina-jina, wai kuma aka zauna lafiya. Gaskiya yadda ba na goyon bayan ya zuba ido kishiya na wahalar da diyar jama'a bai iya yin komai, haka ba na goyon bayan wasu su zane mijin yayarsu, na san in ma wannan ya kawo zama lafiya a wani gidan, tabbas zai iya hada ƙaramin yaƙi a wani, ba wata maganar kishi yanzu maganar maza ce. Ko ma ba haka ba dukan da za su yi min ita ce za ta saka na hana kishiyarta ta cutar da ita? Ko ita ce za ta tunatar da ni ƙimarta da yadda 'yan uwanta suke ƙaunarta don haka dole ta zauna lafiya uwargidar? Kawai dai maza su ji tsoron Allah, in ka san ba za ka iya kula da diyar mutane ba ka barta a gaban uwayenta.

A nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments